Rundunar sojan Nijeriya ta musanta rade-radin da ake yi mata cewa tana yunkurin yin juyin mulki ga zababbiyar gwamnatin shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Rundunar ta bayyana wannan rade-radi a matsayin “labari na karya” wani rahoto da wata jaridar yanar gizo da ba (LEADERSHIP HAUSA) ba ta wallafa a ranar Lahadin da ta gabata, kan zargin yunkurin yin juyin mulki a Nijeriya a sakamakon halin matsi da takura da tabarbarewar tattalin arziki da kasar ke fuskanta yanzu haka.
Idan dai za a iya tunawa, kwanaki, babban hafsan sojojin kasa na Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya gargadi mutanen da ke kira da a yi juyin mulki a kan halin matsin tattalin arziki da kasar ke ciki, ya kuma ja kunne kan masu yadawa da su daina yada irin wannan kalaman.
An samu wata jaridar yanar gizo, ta rawaito wani rahoto cewa an sanya wa rundunar tsaron fadar shugaban kasa cikin shirin ko-ta-kwana, a sakamakon wani yunkuri da ba a saba gani ba, wanda ya sa ake zargin yunkurin juyin mulki ne a Nijeriya.
Ta ce ta samu labarin ne kawai a ranar Lahadin da ta gabata cewa, zargin ya sa gaggawar da ta hada da Kwamandan Rundunar Sojojin Shugaban Kasa, Kanar Adebisi Onasanya da Shugaba Tinubu da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila.
“An sanya Brigade na Shugaban Kasa a cikin shirin ko-ta-kwana bayan wani yunkuri da ba a saba gani ba ya haifar da zargin juyin mulki.
“A makon da ya gabata, Kanar Onasanya ya gana da shugaban kasa da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin kasar sau biyu cikin sa’o’i 20.
Duba Nan: An Bayyana Peter Bai Bar LP Ba
“Sun kuma sanya wasu manyan runduna a karkashin kulawa saboda shirin zanga-zangar,” in ji wata majiyar fadar shugaban kasa ta yanar gizo.
Ita ma kungiyar kwadago a Nijeriya (NLC) na shirin gudanar da zanga-zanga ta kwanaki biyu a fadin kasar, wadda za a yi a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a halin yanzu.
Source: LEADERSHIPHAUSA