Shugaban hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, Abba El-mustapha, ya bayyana cewa, hukumar ta hana Sayarda Littafin Queen Primer kuma hanin ya fara nan take.
El-Mustapha ya bayyana cewa, hukumar a karkashin jagorancinsa ta kama kwafi fiye da 1,200.
ya kara da cewa, Babban dalilin dakatar da Sayarda Littafin shi ne, korafe-korafen da aka gabatar wa hukumar cewa, littafin yana bata tarbiyyar yara.
Don haka, daga yanzun, an hana sayarda wannan littafi a duk fadin jihar Kano.
A wani labarin na daban mutanen da iftila’in ya shafa, a yanzu haka sun samu mafaka a makarantar sakandare ta je ka ka dawo ta GDS da ke yankin Limawa-Jimeta, a Yola babban birnin jihar.
Shugaban makarantar Musa Hassan Jada ya bayyana cewa, mutanen da abin ya shafa sun tare a ajujuwa bakwai na makarantar.
Kazalika, mataimakin gwamnan jihar Kaletapwa George Farauta, ya ziyarci Unguwan Tana domin duba irin barnar da ambaliyar ruwan ta janyo.
Bugu da kari, George ya yi alkawari gwamnatin jihar, za ta kawo masu dauki domin a rage masu radadin zafin aukuwar iftila’in na ambaliyar ruwan.
Amabilayar ruwan dai ta auku ne sanadiyyar cikar da kogin Benuwe ya yi biyo bayan yin ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da kuma sako ruwan Dam na Lagdo da ke a jamhiriyar Kamaru.
Source LEADERSHIPHAUSA