Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour ya yi alkawarin amfani da albarkar kasar noma da Allah ya yiwa Arewa wajen amfanar da kasar nan.
Tsohon gwamnan na Anambra ya ce zai zuba kudaden Najeriya a yankin Arewa don habaka fannin noma.
A fahimtarsa, yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ci gaban Najeriya shi ne babban abin da ya fi mai da hankali a kai.
A wani batu mai daukar hankali, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya bayyana cewa, zai yi duk mai yiwuwa wajen amfani da albarkar da Allah ya ajiye ta kasar noma a Arewacin Najeriya don ci gaban kasa.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust ta wallafa, kamar yadda Legit.ng ta tattaro.
A cewarsa, yankin Arewacin Najeriya na da kasar noma mai girma, inda ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta zuba hannun jari a fannin.
Abin da Peter Obi zai yi idan ya gaji Buhari
Ya shaidawa Daily Trust cewa:
“Muna da kasa mai girma a Arewa da idan aka zuba hannun jari kuma aka noma ta yadda ya dace, Najeriya za ta sauya.
“Adadin mutanen da ya cire daga talauci, adadin wadanda zan raba da batun aware, kuma shi ne adadin da zan rage na ta’addanci. ”
Zan gana da mutane a Arewa, zan gana da mutane a ko’ina sannan na ce su zo, mu zama ahali.
Ina son ‘yan Najeriya su yi alfahari da cewa su ‘yan Najeriya ne.
“Abin da muke dashi a yanzu shine, muna da kasa mai suna Najeriya, amma ba mu da ‘yan Najeriya. Ina so na dawo da ‘yan Najeriya.”
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana manufarsa ta siyar da matatun mai Najeriya ga ‘yan kasuwa idan aka zabe a 2023.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da gidan rediyon Amurka (VOA Hausa) a ziyarar da ya kai birnin Washington DC ta kasar Amurka.
Ya bayyana cewa, matsayarsa game da batun siyar da matatun mai ba sabon lamari bane, domin a cewarsa ya sha fadin inda ya dosa, Daily Trust ta ruwaito.
Source:legithausang