Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban kasa a 2023 ya nesanta kansa da Hoto da aka hangesa kan dardumar Sallah.
Peter Obi ya ce Hotonsa da wasu suka ɗora kan sallayar Sallah ba dai-dai bane ko da kuwa sun yi da kyakkyawar niyya Ana gani Obi ya zarce sauran yan takarar shugaban ƙasa yawan magoya baya a dukkan shafukan aada zumunta.
Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya nesanta kansa da wani hoton daddumar Sallah da aka ɗora Hotonsa, wanda ya fara jan hankali a kafafen sada zumunta ranar Jumu’a.
Vanguard ta ruwaito cewa duk da har yanzun ana kan gudanar da binciken asalin Hoton abun Sallan, Mista Obi, yayin martani kan lamarin ya nesanta kansa da tawagar yaƙin neman zaɓensa daga Hoton.
Ya kuma bayyana cewa har cikin zuciyarsa yana girmama Addinin Musulunci da Musulmai kamar yadda ya ke girmana kowane Addini kuma a ko wane hali ba zai ci mutuncin kowane Addini ba.
“Sanya Hoto na kan daddumar Sallah ba dai-dai bane ko da kuwa an yi da kyakkyawar niyya. Ba shi da alaƙa da tawagar yaƙin neman zaɓe na, ina matuƙar girmama Addinin Musulunci da sauran Addinai.”
An matsa wa Fasto lamba kan Peter Obi A wani cigaban kuma, babban Faston cocin Covenant Christian Nation, Poju Oyemade, ya sha matsin lamba bisa tilas ya goge rubutun da ya yi wanda ya caccaki matasan Najeriya da ke goyon bayan Peter Obi.
Masoyan Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, a yanzu su suka fi shahara a kafafen sada zumunta baki ɗaya daga cikin dukkan yan takarar shugaban ƙasa a 2023.
Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa Fasto Oyemade, a rubutunsa wanda ya goge daga baya, ya ayyana goyon bayan da Obi ke samu a Intanet da, “Ɓata lokaci kan aikin da ba’a shirya ba.”
A wani labarin kuma Hadimin gwamnan PDP da dandazon magoya baya sun sauya sheƙa zuwa APC, tsohon shugaba ya karɓe su Tsohon shugaban APC na ƙasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya karɓi tsohon mashawarcin gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo kan harkokin siyasa, Ogljo Asein, zuwa jam’iyyar APC.
Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Edo, ya yi kira ga ‘ya’yan APC a faɗin jihar su haɗa kai wuri guda domin jam’iyyar ta cigaba da mulkin Najeriya a 2023, kana ta kwace mulkin Edo daga hannun PDP.