Wasu mambobin babban jam’iyyar hamayya ta PDP sun yi korafi kan kashe naira miliyan 12 daga kudin sayar da fom don gina bandaki uku.
Sun yi wannan korafi ne cikin wani sako da aka wallafa a wani dandali na WhatsApp, ‘Concerned PDP Vanguard for Change’ Masu korafin sun nuna cewa ba za su amince shugaban jam’iyyar.
Sanata Iyorchia Ayu ya zubar wa jam’iyyar da mutunci tare da karya lagwon mambobin kamfen din shugaban kasar su.
Amfani da kimanin naira miliyan 12 don gina bandaki guda uku ya kara ta’azzara rikicin jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, The Punch ta gano a ranar Talata.
An ce an samu kudin ne daga sayar da fom a yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar don zaben shekarar 2023.
Duk da cewa wani jami’i na jam’iyyar na kasa aka bawa kwangilar, majiyoyi sun ce lamarin ya janyo rabuwar kai a jam’iyyar.
Majiyoyi sun ce wasu mataimakan shugaban jam’iyyar na kasa sun fusata kan lamarin suna juyayin dalilin da yasa za a kashe wannan kudin kan bandaki uku.
The Punch ta samu kwafin sakon korafin kan kwangilar da ta janyo hayaniya daga dandalin whatspp na ‘Concerned PDP Vanguard for Change’.
Sanarwar korafi kan kashe N12m don gina ban daki 3 da PDP ta yi Sakon da aka aike wa masu ruwa da tsaki, NEC, BoT da dukkan jiga-jigan PDP an masa lakabi da “Naira miliyan 12 daga kudin fom na yan jam’iyyar da ke gwagwarmaya da aka kashe kan bandaki uku, hakan na nufin N4 miliyan kan kowanne bandaki.”
Sakon ya ce: “Dukkan ku za ku yi shiru ne kan wannan da wasu rashawa, amfani da ofis ba bisa ka’ida ba, raba kawuna a NWC da Sanata Ayu ke yi?
“PDP din da muka sani karkashin tsohon shugaban kasa Obasanjo da Jonathan jam’iyya ce da Ministoci ke murabus idan an zarge su da rashawa; jam’iyyar da aka kai kakakin majalisar tarayya Dimeji Bankole kotu kan rashawa karkashin gwamnatin PDP.”
PDP a matsayin ta na jam’iyya ba ta lamuntar rashawa, musamman idan ya fito fili. Jam’iyyar ba ta wasa da mutuncinta a idon jama’a.”
Sanarwar ta cigaba da cewa: “Don haka wane irin PDP muke da shi yanzu da makiya PDP da dan takarar shugaban kasar mu ke murna game da rashawa da cin zarafin Ofis da Ayu ke yi?
“Mambobi suna son dan takarar shugaban kasar mu ya ci zabe.
Mun yi wa PDP bauta sosai ta yadda ba za mu bari mutum daya ya taho ya kashe zuciyar mambobin kwamitin kamfen din shugaban kasarmu ba.”
Rikicin PDP Ya Kara Tsananta, ‘Yan’Yan Jam’iyyar Sun Barke da Zanga-Zangar ‘Ayu Must Go’ a Katsina.
Gamayyar kungiyar matasan PDP a arewa a sun gudanar da zanga zanga a kofar shiga garin Katsina a ranar Lahadi, suna masu neman Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya sauka.
Fusatattun matasan, wadanda ke dauke da kwaleyen rubutu iri-iri, sun ce lallai sai an.
cire Ayu daga kujerar mulki kafin zaben 2023.
Source:legithausang