Yan majalisar dokokin jihar Oyo takwas (8) na jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP, da wasu jiga-jigan jam’iyyar a jihar na gab da sauya sheka jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Daya daga cikin yan majalisar ta PDP, wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana hakan ranar Lahadi a garin Ibadan, birnin jihar, rah rahoton Vanguard.
Ya laburta cewa suna shirin sauya sheka ne saboda jam’iyyar ta hanasu tikitin takara a zaben 2023.
Wannan lamarin ya biyo bayan sauya shekar da mataimakin Gwamnan jihar, Rauf Olaniyan, yayi daga PDP zuwa APC. Bayan rashin mataimakin gwamna, Jam’iyyar PDP za tayi rashin Yan majalisa 8 da jiga-jigai a Oyo.
A wani labarin na daban kuma gawamnatin Zamfara ta sanar da yanke shawarar baiwa al’ummar jihar damar mallakar bindiga domin kare kansu daga hare-haren ‘yan ta’adda.
Cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai mai dauki da sa hannun kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara, gwamnatin Zamfara ta ce ofishin kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ne zai tantance mutanen da suka cancai mallakar bindigogin don kare kansu, musamman manoma dake a yakunan karkara.
Sanarwar ta kara da cewa za a kafa cibiyar tattara bayanan sirri kan ayyukan masu taimakawa ‘yan bindiga da bayanai.
Gwamnatin Zamfaran ta kuma umarci majalisar dokokin Jihar da ta gaggauta nazartar dokar hukunci mai tsauri kan duk wanda aka kama da laifin taimakawa ‘yan ta’adda da bayanai.
Daga karshe ta kuma gargadi mutane da su tabbatar da gaskiyar dukkanin wasu bayanai da za su gabatarwa gwamnati kan wadanda suke zargi da atimakawa ‘yan bindiga, domin kaucewa tafka kura-kurai.
Zalika duk mutumin da ya ba da bayanan da ba sahihai ba kan wani, to fa za a yi masa hukunci iri daya tare da maitaimkawa ‘yan bindiga da bayanai.