Hukumar zaben Najeriya INEC ta bayyana Abiodun Oyebanji, dan takarar jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Ekiti da aka yi a jiya Asabar.
Kwamishinan hukumar zaben mai zaman kanta na jihar ta Ekiti, Farfesa Kayode Oyebode ne ya bayyana sakamakon da misalin karfe 3 na daren jiya wayewar garin yau Lahadi.
Bayan kammala kidaya kuri’un da aka kada, sakamakon ya nuna cewar, Oyebanji, wanda ya samu nasara a kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar Ekitin, ya samu kuri’u 187,057.
Segun Oni dan takarar jam’iyyar SPD ne ya zo na biyu da kuri’u 82,211, yayin da Bisi Kolawole na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 67,457.
‘Yan takara 16 ne suka fafata a zaben na ranar Asabar, inda aka kada jumillar kuri’u dubu 360,753, sai dai dubu 8,888 basu karbu ba.
A wani labarin na daban kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyya mai mulkin Najeriya APC a zaben dake tafe a 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce ya mika sunan wanda ya zaba a matsayin mataimakinsa, ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC.
Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ba kuma tare da ya bayyana sunan da ya gabatar ba.
Kafin wannan lokaci dai Tinubu ya zabi Alhaji Kabir Ibrahim Masari daga jihar Katsina ne a matsayin wanda zai tsaya takarar mataimakinsa domin ya cika wa’adin da hukumar INEC ta kayyade.
Sai dai an tsayar da Masari takarar ne na wucin gadi ne har zuwa lokacin da za a kammala tuntubar juna tsakanin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC, kan wanda za a tabbatarwa takarar.