Rundunar yan sanda reshen jihar Osun ta musanta raɗe-raɗin da ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta cewa an farmaki Ayarin ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu a ƙarshen makon nan.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa rundunar ta musanta jita-jitar ne a wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola, ya fitar.
Ya bayyana cewa labarin da Bidiyon da ake yaɗa wa ake jingina shi ga Ayarin Tinubu ba na yanzu bane, farmaki ne da aka kaiwa ayarin gwamna Oyetola lokacin zanga-zangar EndSARS ranar a watan Oktoba, 2020.
Sanarwan tace: “An jawo hankalin hukumar yan sanda kan wani labari da Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta mai nuna cewa matasan Osun sun farmaki ayarin Sanata Bola Tinubu ranar 8 ga watan Oktoba, 2022.”
Kada ka bari komai ya wuce ka “Hukumar yan sanda na sanar da ɗaukacin al’umma cewa labarin da Bidiyon wani hari ne da aka kai wa.
Ayarin gwamnan Osun, Oyetola Adegboyega, lokacin zanga-zangar EndSARS shekara biyu da suka gabata, 17 ga Oktoba, 2022.”
“Kwamishinan yan sanda, Olawale Olokode, na sanar wa mutane cewa labarin ba haka yake ba kuma ya saɓa, wanda wasu gurbatattun mutane ke yaɗa shi da nufin ta da hankula.”
“Kai tsaye kan batun, Ina mai sanar muku da cewa Sanata Bola Ahmed Tinubu, bai zo jihar Osun ba, babu wani taro da ya halarta.”
Source:legithausang