Mambobin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) a ranar Litinin sun sake zaban Farfesa Emmanuel Osodeke a matsayin shugabansu na kasa ba tare da wata hamayya ba domin ya jagoranci harkokin kungiyar na tsawon wasu shekaru biyu masu zuwa.
Kazalika, kungiyar ta kuma sake zabin Farfesa Chris Piwuna na kwalejin koyar da ilimin likitanci a jami’ar Jos, a matsayin mataimakin shugaban kungiyar na kasa.
Jagororin sun samu wannan zarafin ne a yayin zaben kungiyar karo na 22 da ya gudana a jami’ar Jos ta jihar Filato tsakanin ranakun 19 zuwa 21 na watan Mayun 2023.
Sauran manyan mukaman da kungiyar ta sake zaba sun kunshi: Farfesa Siji Sowande a matsayin ma’aji: Farfesa Ade Adejumo aka zaba a matsayin sakataren kudi; Dakta Austen Sado (Sakatare); Drakta Adamu Babayo (Mai bin diddigin kudaden) da kuma Dakta Aisha Bawa da ta maye gurbin Dakta Stella-Maris Okey a matsayin sakataren walwala da jin dadin mambobi.
Osodeke da take jawabi bayan taron, ya misalta zaben a matsayin wanda aka gudanar bisa nagarta da kwanciyar hankali.
Ya ce za su fitar da cikakken sanarwar manema labarai kan taron nasu da kuma sake zabin nasa da sauran manyan mukaman da aka yi idan suka koma Abuja.
A wani labarin na daban Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa da su mika takardunsu na ajiye aiki daga yanzu zuwa ranar Juma’a 26 ga Mayu, 2023.
Masu rike da mukaman sun hada da kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, manyan jami’an gudanarwa na kamfanoni mallakar gwamnati, babban mataimaki na musamman, mataimaka na musamman, ma’aikatan hukumomin gwamnati.
Wata sanarwa da ta fito daga babbar sakatariya a ofishin sakataren gwamnatin jihar, Bilikisu Shehu Maimota, ta fitar a ranar Litinin din nan, ta umurce su da su mika aiyukansu ga manyan sakatarori ko daraktocin gudanarwa na ma’aikatun gwamnati.
“Wannan ya yi daidai da tsarin da aka kafa domin wa’adin mulki na biyu na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai cika a ranar 29 ga Mayu, 2023,” cewar sanarwar.