Kwanan baya, jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya Cui Jianchun ya gana da dalibin kasar Nijeriya Prosper Dania Oshoname a ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Nijeriya, inda ya taya shi murnar samun lambar yabo ta matsayin farko wato lambar yabo ta “Tianhe” cikin gasar zane-zane mai taken “Mafarkina”. Kuma, an aika zanensa mai taken “fatanmu” zuwa tashar sararin samaniya ta kasar Sin tare da kumbo mai dauke da mutane na Shenzhou-16 a ranar 30 ga watan Mayu.
Jakada Cui ya nuna yabo matuka ga dalibi Prosper Dania Oshoname, ya ce, dalibin ya kasance kyakkyawar wakili cikin matasan kasar Nijeriya, ya taba samun lambobin yabo da dama cikin gasar zane-zanen da ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Nijeriya ya shirya, ya kuma nuna kwarewarsa a wannan fanni saboda da kokarin da ya yi.
A watan Maris na bana, ofishin sakatare na kwamitin aiwatar da ayyuka bayan dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka, da ofishin kula da ayyukan sararin samaniya mai dauke da mutane na kasar Sin da ofisoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen Afirka, sun yi hadin gwiwa wajen gabatar da gasar zane-zane mai taken “mafarkina” ga matasa da yaran nahiyar Afirka. Cikin wannan gasa, zane-zane guda 10 daga cikin guda 2000, sun lashe lambobin yabo, cikin har da zanen da Prosper Dania Oshoname ya yi. Kuma, an kai wadannan zane-zane zuwa tashar sararin samaniya ta kasar Sin domin yin nune-nune. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)