Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana dan takarar da zai so goyawa baya a zaben shugaban kasa na 2023.
Ortom ya ce ba don shi dan PDP bane da zai yi kokarin ganin Peter Obi na jam’iyyar LP ya zama magajin Buhari.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba, yayin da ya sa labule da tsohon gwamnan na jihar Anambra.
Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana cewa ba don shi dan PDP bane da babu abun da zai hana shi aiki don ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya lashe zabe mai zuwa.
Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba, yayin da ya karbi bakuncin tsohon gwamnan na jihar Ana,bra a gidansa da ke Abuja, Channels TV ta rahoto.
Ortom ya ce: “Ni dan PDP ne kuma PDP nake yiwa aiki amma bari na fada maku da ace ba a PDP nake ba, da kun gan ni ina yiwa Peter Obi aiki amma a PDP nake.
“Bari muga yadda abubuwa zasu kasance amma magana ta gaskiya ita ce cewa littafin bibul ya ce mutum baya iya samun komai face abun da aka bashi.”
Ortom ya ce ba lallai ne ace Obi na da abubuwan bukata ba, amma idan Allah ya zartar da hukunci, babu wanda ya isa ya hana shi.
Ya kuma bukaci Atiku, Obi da Tinubu da su hadu sannan su amince da daya daga cikinsu, rahoton Vanguard.
Gwamnan na Benue wanda ya kasance na hannun damar Gwamna Nyesom Wike yana daya daga cikin gwamnonin PDP da suka ce lallai sai shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus daga kujerarsa.
Ya bayyana Obi, Bola Tinubu na APC, da Atiku Abubakar na PDP a matsayin manyan yan takara sannan ya bukaci yan Najeriya da su zabi wanda yafi cancanta a tsakaninsu ba tare da son zuciya ba.
Har yanzu dai ba a gane inda tsagin Wike suka sanya gaba ba domin dai ba a ganinsu a wajen gangamin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP.
Hakan ya sanya mutane dasa ayar tambaya kan ko zasu marawa wani dan takara na daban baya maimakon dan takarar jam’iyyarsu a zaben 2023 mai zuwa.
Source:legithausang