Omoyele Sowore ya jerowa SERAP kadarorin da ya mallaka da kuma kudin da yake da shi a asusun bankinsa.
‘Dan takaran Shugaban kasar ya ce abin da ke bankinsa bai wuce N5000 ba, sai gidaje biyu da kuma motocin sa.
A yunkurin kungiyar SERAP na ganin masu neman shugabancin Najeriya sun bayyana kadarorin da suke da shi, Omoyele Sowore ya ba su amsa.
Ta shafin Twitter wannan kungiya ta SERAP mai zaman kanta, ta nemi Omoyele Sowore ya wallafa bayanin arzikinsa a fili, tuni ya jero iyakar arzikinsa.
10 ‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar AAC ya yi bayanin motocin da yake da su, da gidansa a kauye da wayoyin salula da kamfani da gida a kasar Amurka.
Omoyele Sowore ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta rufe masa akawun dinsa da ke banki tun tuni.
Me Sowore yake da shi?
“Ina da motoci biyu da aka hau; Toyota Camry & Lexus RX 350, sai gida a kauyenmu wanda watakila darajarsa ta kai Naira miliyan 5.
Ina da wayoyin iPhone uku da Galaxy Note 10 Lite (idan har za a iya kiransu kadarori), sai kamfanin SaharaReporters Media Group Tare da gida mai daki hutu a birnin New Jersey (a Amurka), bayan wannan ba ni da komai!”
An rufe mani akawun “Gwamnatin tarayya ta rufe asusun bankuna na tun 2019 bayan an kama ni saboda na jagoranci zanga-zangar #RevolutionNow a Agustan 2019 Akwai N4,800 a asusun GTBank da na ke da shi a Najeriya kafin a cafke ni.
Nayi kokari na bude asusu da Bankin Kuda da N463 da yamman nan.”
SERAP ta bukata, ‘dan takaran na 2023 ya fadawa Duniya cewa sam bai goyon bayan sayen kuri’u da ‘yan takara da jam’iyyu suke yi a kasar nan.
Sayen kuri’u Sayen kuri’un talakawa yana cikin matsalolin da ake fuskanta wajen gudanar da zabe a Najeriya. Sowore ya yi tir da wannan danyen aiki da aka shigo da shi.
Da aka nemi bayanin arzikinsa, ‘Dan takaran Shugaban kasa, Yele Sowore, ya ce abin da ke bankinsa bai wuce N5000 ba, sai gidajensa biyu da motoci.
Abokin takarar Tinubu, Kun ji labari Bishof Igbokwe Prince yana ganin abin da jam’iyyar APC ta yi na tsaida Musulmai a 2023, saboda ta lashe zabe ne ba domin kishin addini ba.
Babban Limamin Majami’ar Yoke Breaker Prophetic Ministry ya bijirewa CAN, ya je bikin kaddamar da Kashim Shettima da jam’iyyar APC ta yi a Abuja.
Source:hausalegitng