Zargin rashawa ya janyo rikicin shugabanci a kungiyar neman kafa kasar Yarbawa mai suna Ilana Omo Oodua Worldwide.
Wale Adeniran, jagora kuma shugaban kungiyar, ya sanar da murabus dinsa domin bada daman a yi sahihin bincike kan zargin.
Jagoran na kungiyar kafa kasar Yarbawa ya kallubalanci duk wani da ke da hujja a kansa ya taho ya nuna wa al’umma.
Wale Adeniran, jagora kuma ciyaman din masu neman kafa kasar Yarbawa, wacce aka fi sani da Ilana Omo Oodua Worldwide, ya yi murabus daga matsayin sa a kungiyar kan zargin rashawa da almubarazanci.
Adeniran ya sanar da murabus dinsa a wani bidiyo da aka dora a shafin YouTube, mai suna Omoboriowo media, a ranar Asabar 7 ga watan Janairu.
Jagoran na Yoruba Nation ya sauka daga mukaminsa ne domin ya bada dama a yi sahihin bincike kan zargin damfara da aka masa.
Adeniran ya kallubalanci duk wani da ke da hujja a kansa ko wani da ya tura wa kungiyar kudi ta hannunsa ya taho ya bayyana wa al’umma.
Ya yi kira ga shugabannin yarbawa su kafa kwamitin don bincikar zargin da ake masa. Kalamansa: “Ina son yin amfani da wannan damar don sanar da sauka na daga shugabancin Ilana Omo Oodua Worldwide, a matsayin mamba na Ilana Omo Oodua Worldwide, na sauka ne don bada damar a yi bincike kan zargin da ake min.
“Saboda a dukkan kasashen da suka cigaba, abin da suka saba yi shine idan an zargi mutum mai mukami, zai ajiye aiki don bada dama a yi bincike, abin da na yi kenan yanzu.
“Na gode muku, kuma duk abin da binciken ya haifar, za a sanar da al’umma.
Bai kamata a boye ba. Za a bayyana sakamakon binciken don kowa ya san gaskiya kan zargin rashawa da damfara da ya shafi wannan gwagwarmayar namu.
Nagode muku.”
Source:LegitHausa