A taron na cibiyar Olusegun Obasanjo an gayyaci Sanusi II a cikin wadanda suka yi jawabi ta yanar gizo Muhammad Sanusi II ya yi tir da yadda ake saba dokar zabe ta hanyar sayen kuri’un mutane.
Sarkin Kano na 14, Malam Muhammad Sanusi II ya bayyana sayen kuri’u a matsayin wani sharri da ya zama barazana ga tsarin siyasar kasar nan.
Daily Trust ta ce Mai martaba, Muhammad Sanusi II ya yi jawabi ne a wajen wani taro na musamman da cibiyar dakin karatun Olusegun Obasanjo ta shirya.
Muhammad Sanusi II ya na ganin sayen kuri’a yana kawo babban cikas wajen zaben shugabanni.
Taron da aka gudanar ta yanar gizo ya tattauna ne a kan abin da ya shafi kafofin sada zumunta na zamani da kuma sha’anin rashin tsaro da zabe a Najeriya.
A jawabin na sa, Sanusi II yake cewa sayen kuri’u da aka fito da shi a lokacin kada kuri’a, raina dokar zabe ne, sannan rashin sanin darajar akwatin zabe ne.
Mutane na saida ‘yancinsu Khalifan na Darikar Tijjaniya a Najeriya ya nuna takaicinsa a game da yadda mutane suke nunawa Duniya takardar zabensu bayan sun kada kuri’arsu a sirri.
Wasu mutanen suna yin hakan ne domin ya zama shaida gaban ‘yan siyasa, su gamsar da su cewa sun zabe su domin a biya su kudin kuri’ar da suka bada.
Akwai gyara a dokar zabe Duk da an inganta dokar zabe, Basaraken yana ganin akwai bukatar al’ummar Najeriya su yi kira ha hukuma da su tabbatar da an yi adalci da kuma gaskiya.
“Daya daga cikin hanyar da ake murde zabe a sabuwar dokar zabe ita ce tsarin sayen kuri’a, kuma wannan rashin bin dokar sirrinta kuri’a ne.”
”Dole mutanen Najeriya da al’mma su tashi-tsaye, su tabbatar da sirrin kuri’arsu da tabbatar sirrin zabin da suka yi a lokacin da ake yin zabe.”
“Muna bukatar mu tabbatar da cewa wadanda suka shiga ofis, su ne wadanda muka zaba.”
Muhammadu Sanusi Rasuwar Bashir Tofa A farkon shekara nan ne aka samu rahoto Mai martaba Muhammadu Sanusi ya yi wa jama’ar Kano da Arewa ta’aziyyar rashin Alhaji Bashir Othman Tofa.
Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yace mutuwar Dattijon rashi ne ga Najeriya gaba daya, Sanusi II ya ce Marigayin ya nunawa danginsu kauna.
Source:hausalegitang