Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar Adawa, PDP a zaben 2023, Ifeanyi Okowa, ya jagoranci karbar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa PDP a Sakkwato tare da bayyana cewar lokaci ya yi da za su ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta.
Mataimakin Atiku Abubakar a 2023, ya jaddada cewar canza shekar fitattun ‘yan siyasar daga jam’iyyar da ke mulkin kasa zuwa jam’iyyar adawa a karkashin jagorancin, gwamna jihar Aminu Waziri Tambuwal, babbar alama ce ta samun nasarar PDP kamar yadda ya bayyana a yammacin ranar Lahadi a Sakkwato.
Okowa ya ce a shekara mai zuwa mulkin Nijeriya zai koma a hannun jam’iyyar PDP wadda za ta kawar da matsalolin al’umma da inganta jin dadinsu.
Kana ya ce PDP za ta dawo da kima da martabar Nijeriya a idanun duniya.
Ya ce a yanzu lokaci ne na ceto Nijeriya kuma lokacin sake gina kasa, don haka ya zama wajibi a yi aiki tare domin kubutar da Nijeriya daga hannun wadanda ke kokarin ruguza ta.
“Ya bayyana tare da cewar a bisa ga kwarewa da gogewa da sanin makamar shugabancin da Atiku Abubakar yake da ita zai jagoranci mulkin da kowa zai yaba a Nijeriya.”
Kusoshin ‘yan siyasar wadanda fitar su ta girgiza APC tare da karya lagonta a Jihar sun hada da uku daga cikin wadanda suka tsayawa jam’iyyar takarar fidda gwani na zaben gwamna, wato tsohon Ministan Wasanni kana Daraktan yakin neman zaben Buhari a 2019 a Sakkkwato, Yusuf Sulaiman, Shugaban Kwamitin Yaki da Fatara a Majalisar Wakilai, Hon. Abdullahi Salame da A.A Gumbi.
Haka ma akwai Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Sakkwato, Hon. Aminu Achida da tsohon Ministan Al’adu, Sanata Bello Jibril Gada da kuma Hon. Yusuf Kurdula wanda ke wakiltar Tangaza/Gudu a Majalisar Wakilai.
Sauran sun hada da Hon. Murtala Maigona, wanda ke wakiltar Karamar Hukumar Wamakko a Majalisar Dokoki ta Jiha da tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Sakkwato ta Arewa da Binji, Abdullahi Hassan da Sayyadi Nuhu Binji da tsofaffin kwamishinoni Aminu Bello Sokoto da Dahiru Maishanu Yabo.
Sai Mataimaki na Musamman ga Sanata Aliyu Wamakko kan Yada Labarai, Hassan Sahabi Sanyinnawal, da Yahaya Dallatu da ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ‘yan kwangila da dubban daruruwan magoya bayansu.
A jawabinsa, tsohon Ministan Wasanni, Yusuf Sulaiman, ya bayyana cewar canza shekarsu daga APC zuwa PDP abin murna ne kuma za su jajirce domin ganin PDP ta samu nasarar kafa gwamnati daga sama har kasa baki daya.
Ya ce 2023 lokaci ne da jam’iyyar PDP za ta sake komawa fadar mulkin kasa.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a takaitaccen jawabinsa, ya bayyana cewar a bisa ga kasawar APC na magance matsalolin da suka dabaibaye Nijeriya, wajibi ne a 2023 al’umma su zabi PDP domin kai kasar nan a tudun mun tsira.
Ya ce APC ba ta da tsari da cancantar da za ta kawar da matsalolin ‘yan Nijeriya.
Ya ce sakon da fitar manyan ‘yan siyasar ke nunawa a bayyane yake na kyakkyawar makoma da ke a gaban PDP wadda ya ce ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen shimfida ingantaccen mulki na gari wanda ‘yan Nijeriya za su yaba a karkashin jagorancin Wazirin Adamawa.