Tsohon babban sakataren hukumar jami’o’i na kasa (NUC), Farfesa Peter Okebukola, ya ce, zargin magundin jarrabawa da ake zargin daliba, Ejikeme Joy Mmesoma, ya zama izina ga harkar zana jarrabawar manyan makaraantun da ke kasar nan.
Okebukola wanda ya daganta abinda dalibar ta aikata da abin takaici, inda ya shawarci hukumomin manyan makarantu da ke a kasar nan da su rungumi tsari da dabarun zamani na Oloyede, don kawo karshen aikata magudin jarrabawa a makarantun kasar nan da makaratun gwamnati.
Ya ce, mutane da dama na sane da yadda magatakardar hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ke yin kokarin tabatar da ganin an tabbatar da gaskiya wajen zana jarrabawar JAMB.
Daliba Mmesoma dai, ta yi ikirarin cewa, ta samu maki 362 na sakamakon jarrabawar UTME da dalibai suka zana a 2023, inda aka yi ta murnar samun wannnan makin nata a matsayin wadda ta fi kowanne dalibin da ya zana jarrabawar samun maki.
JAMB dai ta yi zargin cewa, sakamakon jarrabawar da Ejikeme ta yi ikirarin samu na bogi ne, wanda ta zarge da sauya samakakon daga makin da ta samu na 249, inda hakan ya janyo cece-kuce da mayar da martani daga wasu al’umar kasar nan.
A wani labarin na daban hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wata mahajjaciya mai suna Hadiza Isma’il, yar asalin karamar hukumar Madobi a kasar Saudiyya.
Hadiza Isma’il, ta rasu a ranar Litinin da misalin karfe 3:15 na rana agogon Saudiyya, bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda sanarwar shugaban tawagar manema labarai na Hajjin bana fitar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
Sanarwar ta ce, an kai matar mai shekaru 58 a asibitin NAHCON domin jinyar zazzabi kafin a kai ta asibitin Sarki Abdulaziz da ke Makkah inda aka tabbatar da rasuwarta.
Tuni dai aka binne ta a garin Makkah bayan yi mata sallar jana’iza a masallacin Haramin Makkah.
Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai na Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu Danbappa ya mika sakon ta’aziyyarsa a madadin hukumar da Gwamnati ga iyalan mai rasuwar, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama, ya kuma baiwa iyalai hakurin rashinta.