Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi Allah wadai da rahoton da ke cewa an kashe akalla yan arewa 100 a yankin kudu maso gabas cikin mako daya.
Sakataren labaran kungiyar Inyamuran, Alex Ogbonna, ya bayyana rahoton a matsayin kanzon kurege mara tushe balle makama.
Ohanaeze ta yi kira ga kama wadanda suka kokan sannan ta bukaci hukumar tsaro da ta tabbatar da da ganin sun gabatar da hujjarsu kan rahoton.
Kungiyar kare muradun Inyamurai na Ohanaeze Ndigbo ta yi watsi da rahoton da ke ikirarin cewa an kashe yan arewa fiye da 100 a yankin kudu maso gabas.
A cikin wata sanarwa da kakakinta, Alex Ogbonnia, ya saki, kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin karya mara tushe balle makama, jaridar Vanguard ta rahoto.
Ohanaeze ta yi watsi da batun kashe yan arewa 100 a kudu maso gabas.
A zauna lafiya: Ogbonnia ya yi kira da a binciki rahoton sannan ya bukaci hukumomin tsaro da abun ya shafa su kama wadanda suka kokan don nuna hujja kan irin wannan ikirari.
Kungiyar Inyamuran ta bayyana cewa irin wannan ikirari na iya tayar da kasar sannan kuma cewa bai kamata a yi masa rikon sakainar kashi ba.
Ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da kama wadanda suka yada zargin na karya.
Ogbonnia a cikin jawabin nasa ya bayyana cewa rahoton da ke ikirarin cewa yan awaren IPOB sun kashe akalla yan arewa 100 cikin mako guda yana da matukar damuwa, TVC News ta rahoto.
Rahoton ya nakalto Auwal Abdullahi Aliyu, jagoran kungiyar hadaka ta arewa yana umurtan direbobi daga yankin arewa da su guji zuwa kudu maso gabas.
Wani bangare na jawabin na cewa: “Da farko, karya ne cewa an kashe akalla yan arewa 100 a yankin kudu maso gabas cikin makon jiya.”
“Abu na biyu, Dr. Aliyu da ake magana a kai baya cikin shugabannin arewa mazauna kudu maso gabas kuma saboda haka baya da hurumin magana kan dangantakar da ke tsakanin yan arewa da mutanen kudu maso gabas. ”
Abu na uku: Mutum zai fara tunanin manufar da ke tattare da irin wannan karya da yunkurin tada zaune tsaye cewa ”
Akalla yan arewa 100 aka kashe a kudu maso gabas a cikin makon jiya. ”
Abu na hudu: Bincike zai nuna irin bata sunan da hakan zai yiwa Najeriya a tsakanin kwamitin kasashe cewa an kashe mutum 100 cikin mako daya.”