Dakarun ‘yan sanda na reshen jihar Ogun sun kubutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi.
Ana zargin abokan aikin Haruna Usman wajen harkar damfara ne suka dauke shi saboda ya cuce su.
Da aka samo wasu kudi kimanin N26m, a maimakon a raba daidai, sai shi ya tsere da kusan N24m.
Jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Ogun sun ceto wani da ake zargin ‘dan damfara ne, Haruna Usman, wanda abokan aikinsa suka dauke shi.
Rahoton Vanguard ya nuna cewa wasu da suke aikin damfara tare da Haruna Usman ne suka dauke shi a dalilin yaudararsu da ya yi bayan an sato miliyoyi.
An tafka wata damfara ne ta N26,437,950, sai shi Haruna Usman ya dauke duka kudin, ya bar sauran wadanda aka yi aikin da su da N2,200,000 rak.
Ganin wannan mutumi shi kadai ya tashi da 91.7% na abin da suka samu, sai suka yi garkuwa da shi.
Abin da ya faru
‘Yan sanda Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Ogun, SP Abimbola Oyeyemi ya fitar da jawabi inda ya yi bayanin abin da ake zargin ya faru tsakaninsu.
SP Abimbola Oyeyemi ya yi magana a ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba 2022, ya ce a ranar Litinin aka kama ‘yan damfara watau ‘Yan Yahoo hudu.
An kama Agbe Simeon, Messiah Nicky, Oladapo Dolapo da Yetunde Shonola ne a kauyen Orile Imo a karamar hukumar Obafemi Owode a jihar Ogun.
Jami’in yake cewa sun samu labarin an dauke Usman ne a ofishin ‘yan sanda na Owode Egba.
Jaridar Sun ta ce nan take ‘yan sandan suka kai hari, aka yi nasarar cafko mutane biyu daga cikin wadanda suka dauke wannan mutumi, biyu su ka tsere.
Shi kadai ya dauke N24.2 Abin da ya faru shi ne ‘Yan damfaran sun sato N26,437,950 daga wajen wani wanda ba a san shi ba tukuna, sai ya ba sauran ‘yan gungun na sa N2,200,000.
Wannan mutumi da a karshe aka yi awon-gaba da shi bayan an kai shi gidan wani mai maganin gargajiya, ya yi ikirarin ba ayi nasarar sace duka kudin ba.
A nan ‘yan gungun suka yi wa Usman barazanar za su kashe shi idan bai cika masu ragowar kudin ba. Ana haka ne sai rundunar ‘yan sanda suka yi ram da su.
Rahoton ya ce Kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole ya bada umarni a kai maganar zuwa sashen CID domin a cigaba da yin binciken da ya kamata.
Sarki ya yi tsinuwa a Ebonyi
An ji labarin yadda wani Basarake a Ebonyi ya yi tsinuwa, ya ce duk wanda yake adawa da David Umahi wajen zama Sanata, ba zai ga kirismetin shekarar.
Gwamna David Umahi mai shirin barin-gado, ya bayyana muhimman abubuwan da zai sa a gabansa idan ya samu kan shi a majalisar dattawa a Mayun 2023.