Rundunar yan sanda ta jihar Ogun ta ce ta kama wani Adeyemi Babatunde, dan shekara 26, kan kashe wani Obafunsho Ismail, dan shekara 46.
A cewar yan sandan, wanda ake zargin ya yi amfani da motarsa ya bige marigayin yayin jayayya da suka yi a ranar Talata, rahoton The Cable.
Yan Sanda Sun Cafke Wani Saboda Murkushe Wani Da Mota Sakamakon Jayayya Da Suka Yi.
Abimbola Oyeyemi, kakakin yan sandan Ogun, cikin sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, ya ce an fara jayayyan ne bayan Babatunde ya yi amfani da motarsa ya bige Ismail, hakan ya lalata masa danja ta baya.
Bayan hakan, an ce marigayin ya kusanci Babatunde ya bukaci ya sauka daga motarsa ya duba barnar da ya masa.
A cewar Oyeyemi, wanda ake zargin ya ki saukowa daga motarsa kuma ya yi kokarin tserewa.
Amma, an rahoto marigayin ya zauna a bayan motar wanda ake zargin don hana shi tserewa daga wurin.
Sanarwar ta ce: “Wanda ake zargin, Adeyemi Babatunde, daga bisani ya sako ya gargadi marigayin ya sauka daga gaban motarsa idan baya son ya yi asarar ransa.
“Daga nan ya koma motarsa, ya figi motar da gudu hakan yasa marigayin ya fado daga motar kuma motar ta bi ta kansa. ”
Bai gamsu ba, wanda ake zargin ya sake juyowa da motar ya bi ta kan marigayin don ya tabbatar ya mutu. Bayan kammala hakan, ya tsere da motarsa.”
Daga bisani an bi sahunsa an gano shi a gidan mahaifinsa a Kemta Idi a Abeokuta inda aka kama shi a ranar 20 ga watan Disamban 2022.
An kwato motar da aka yi amfani da shi wurin aikata laifin an kai ta caji ofis.