Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, ya tafka babban kuskuren zabar Atiku Abubakar mataimaki a lokacin Wa’adin mulkinsa a 1999.
Obasanjon ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyi a wani taro na wasu dalibai a Abeokuta da ke Jihar Ogun.
Ga wani bangare Daga Cikin hirar Obasanjo da Daliban, kamar yadda jaridar BBC Hausa ta nakalto.
“Ba zan ce bana kuskure ba – Na yi sau da yawa,” in j iObasanjo.
“Amma wani abu da ya faru da ni shi ne Ubangiji bai taɓa kunyata ni ba. Kuma wannan abu ne mai muhimmanci.
“Sakamakon wannan kuskure ne mai kyau, Ubangiji ya kare ni,” in ji Obasanjo.
A wani labarin na daban da safiyar ranar Lahadi ne dakarun Rasha suka harba makami mak linzami zuwa birnin Kyiv na Ukraine, a wani mataki na ci gaba da mamayar kasar.
An jiyo karar ababen fashewa a sassa daban-daban na birnin Kyiv din.
Magajin birnin, Vitali Klitshko, ya ce tuni motocin daukar marasa lafiya hade da ma’aikatan ceto suka isa wurin.
Harin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya sake kira ga aminan Ukraine su kai musu daukin makaman kare sararin samaniyar kasarsa.
A bidiyon da ya ke wallafa a kowanne dare tun bayan fara yakim, Mista Zelensky, ya ce yakin da suke yi da Rasha ya shiga wani mataki mai sosa rai da tsananin wuya, bayan Rasha ta karbe birnin Severodonetsk.
Yakin dai ya faro ne tun a watan Fabrairun 2022, wanda yanzu ya kawo sama da watanni 4 ke nan ana gwabzawa.
Yakin ya yi sanadin rasa rayukan dubban mutane daga tsagin Ukraine da Rasha, ciki har da manyan dakarun sojin kasashen biyu.