Oba Abdulrosheed Akanbi Telu 1 ya saka kafar wando daya da Sarakunan gargajiyar kasar Yarbawa.
Oba Rasheed ya dade yana bayyana cewa babu wani ubangiji sai Allah kuma Sarakuna su daina hada Allah da wani.
Shugaban bokayen kasar Osogbo ya yi masa martani mai zafi, ya ce ya koma Saudiya idan bai so.
Sarkin garin Iwo Oba Abdulrosheed Akanbi, wanda Suruki ne ga Sarkin Kano, Ado Bayero, ya yi kira ga Sarakunan gargajiyar kasar Yoruba su dawo hanyar Allah wajen gudanar da rayukansu.
Oba Akanbi ya bayyana hakan a Iwo ranar Laraba yayinda bikin ranar Ubangiji kamar yadda aka saba shekara-shekara a kasar Iwo, rahoton Punch.
Sarkin ya jaddada cewa duk Sarkin da ke bautar gumaka ba wakilin Allah bane kuma kamata yayi su sauka daga mulki su koma aikin boka.
Yace: “Sauran Sarakunan kasar Yarbawa su yarda da wannan saboda ba zai yiwu su zama wakilan Allah ba sai sun daina aikata shirka.”
“Allah shine Sarkin kowa, kuma duk Sarkin dake Shirka ba wakilin Allah bane a doron kasa. Duk Sarkin dake bautar wani abu ko gunki ya sauka daga mulki ko ya zama boka.”
Ra’ayinsa kan zaben 2023 Game da zaben 2023 mai zuwa kuwa, Sarkin ya ce a mayarwa Allah zabin mutumin da yafi zama alheri ga Najeriya.
A baya dai Sarkin ya nuna goyon bayansa ga dan takarar kujerar shugaban kasan APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Amma Shugaban bokayen garin Osogbo, Araba Awo, Ifayemi Elebuibon, ya ce Sarkin Iwo bai fahimci Sarauta a kasar Yarbawa ba.
Ya fadawa Sarkin ya koma kasar Saudiya a bashi sarauta idan bai son bautan gumaka.
A Landan Yace: “Odu Ifa ya kafa garin Iwo, ba Al-Qur’ani ba.
Oluwo ya koma kasar Saudiyya ya zama Sarki a nan amma ba a kasar Yarbawa ba.
Bai fahimci Sarautar ba.”
Sarkin Iwo ya auri Gimbiyar Kano, Firdausi Ado Bayero A farkon shekarar nan, Sarkin Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi (Telu 1), ya zama surukin masarautar Kano yayin da ya auri Firdaus Abdullahi, wacce jika ce ga marigayi mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.
An daura auren a gidan Madakin Kano.
Source:legithausang