Nyesom Wike bai hakura da maganar kyale Gwamnoni su rika karbar harajin VAT a jihohinsu ba.
Gwamnan ya gabatar da N420bn a matsayin kasafin kudin da Ribas za ta kashe a shekara mai zuwa.
Wike ya yi wannan lissafi ne har da VAT da Gwamnatin Ribas za ta karba, duk da shari’ar tana kotu.
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike yana nan a kan maganar canza tsarin haraji, ta yadda gwamnoni za su rika karbar harajin VAT a jihohinsu.
Nyesom Wike ya yi kira ga sauran Gwamnonin kasar nan, da su taimakawa Ribas wajen ganin jihohi sun karbe iko da harajin kayan masurufi na VAT.
Daily Post tace Mai girma Gwamnan ya yi wannan kira ne a lokacin da ya gabatar da kasafin kudin Ribas na shekarar 2023 a gaban ‘yan majalisar dokoki.
A Matsayin Gwamna Da yake jawabi a ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba 2022, Gwamnan yace kasafin kudin na 2023 ya yi la’akari da kason da Ribas za ta samu daga VAT.
Wike ya fara samun nasara a kotu Ganin Alkalin kotun tarayya ya zartar da hukunci cewa jihohi ke da iko da wannan haraji a Najeriya, Gwamnan ya fara lissafi da kudin a cikin baitul-mali.
A yanzu maganar tana gaban kotun koli, inda za a raba gardama tsakanin bangarorin biyu.
Wike ya yi wa ‘yan majalisar jiharsa bayanin cewa abin da gwamnatin Ribas za ta kashe a shekara mai zuwa, ya ta’allaka da hukuncin da kotun koli tayi.
Rahoton yace Gwamnan ya jaddada cewa zai dage wajen ganin ya bunkasa kudin shiga ta hanyar jawo masu hannun jari, bude kamfanoni da gyara haraji.
Majalisa “Za mu cigaba da zage dantse wajen kokarin mu na kara kudin-shigan da muke samu ta hanyar kawo damammaki, shigo da hannun jari, kamfanoni da gyara karbar haraji.
Duk da ba mu kai ga inda muke hari ba, amma ba za muyi kasa a gwiwa ba a nufinmu na rage dogaron da jihar mu tayi da gwamnatin tarayya wajen tsara kasafin kudinta.
Muna kira ga sauran takwarorinmu jihohi da su bamu gudumuwa wajen wannan gwagwarmaya domin samun damar yankewa da karbar harajin VAT a matakai na jihohi.” – Nyesom Wike.
This Day tace gwamnan ya nuna tun tuni akwai bukatar a canza yadda ake rabon arziki, yace gibin da ake samu a kasafin kudi a dalilin karancin haraji ne.
Wike ya jinjinawa Buhari Kwanan nan aka samu rahoto Gwamna Nyesom Wike ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta biya jihohin Neja-Delta kudin da suke bin bashi.
Jihohin masu arzikin fetur, wanda Gwamnoni suke bin gwamnatin tarayya, bayan an dade ana sauraron kudin, yanzu sun fito.
Source: Legithausa