Reshen birnin tarayya (FCT) na kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), ta yi tir da da Allawadai da kamawa da tsare Edita Mista Ediri Oyibo da Paul Utebor dan rahoton kafar yada labarai ta yanar gizo, TheNewsGuru.com.
Jami’an ‘yansandan shiyya ta 7 da ke babban birnin tarayya Abuja ce ta cafke su.
A wata sanarwar manema labarai da shugaban NUJ a FCT, Mista Emmanuel Ogbeche ya fitar, ya misalta kamen da aka yi wa ‘yan jarida abun da ba za a lamunta ba kuma kamene da aka yi ba tare da amfani da hankali ba.
A cewarsa, an aike da wasikar gayyata ga Oyibo da Utebo domin yin hira da mataimakin kwamishinan ‘yansanda (DCP), da ke kula da sashin binciken manyan laifuka (CID), wasikar mai dauke da kwanan wata 18 ga watan Fabrairun 2023 amma daga bisani kawai aka cafkesu bayan zuwansu.
Ya ce, “Yansandan sun yi ikirarin a cikin wasikar cewa suna binciken wani kes ne na hada baki, bata suna, bada bayanai na karya da barazana kan rayuwa ga su ‘yan jaridan kan labarin haihuwar wani yaro.
“Yan jaridan, wadanda suka shafe tsawon kwanaki hudu a tsare cikin yanayi marar kyau, sannan an ki bada belinsu ba duk da ganawa da aka yi ta yi, sannan an nemi su kawo ma’aikacin gwamnati mai matakin aiki da bai yi kasa da level 14 a matsayin mai tsaya musu ba.
“Abun mamaki, bayan cika sharadin belin, a ranar Juma’a ga watan Fabrairun 24, cikin gaggawa ‘yansandan suka je suka gurfanar da su a gaban kotun majistire a cikin FCT da ke Wuse Zone 6 amma sun samu kotun ba zauna ba. Amma ‘yansandan sun cigaba da tsaresu ta haramtaccen hanya.
“NUJ tana bukatar a gaggauta sake Mr. Ediri Oyibo da Paul Utebor sannan muna neman ‘yansada su cigaba da bin hanyoyin da suka dace wajen gudanar da ayyukan da ke gabansu.”
A wani labarin na daban dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya lashe akwatin mazabar gidan Sarkin Kano da kuri’a 99 a zaben shugaban kasa, yayin da APC mai mulki ta samu kuri’a 39.
A zaben Sanata da aka gudanar a mazabar ta gidan Sarkin Kano, jam’iyyar NNPP ta samu kuri’a 102, APC ta samu kuri’a 53 yayin da kuma jam’iyyar PDP ta samu kuri’a 15.
A zaben ‘yan majalisar tarayya kuwa, NNPP ke kan gaba da kuri’a 99, sai APC ke biye mata da kuri’a 46, PDP ta samu kuri’a 24, yayin da jam’iyyar ADC ta samu kuri’a hudu kacal.
A yanzu haka dai ana ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a yau Asabar.
Source:LeadershipHausa