Hukumar zaɓen jihar Neja, (NSIEC) ta sanar da sakamakon zaɓen Ciyamomin da ya gudana ranar Alhamis 10 ga watan Octoba, 2022.
Sakamakon ya nuna cewa APC ta yi nasara kan sauran jam’iyyu, ta lashe zaɓen Ciyamomi 25 da ke faɗin jihar Neja.
Kwamishinna NSIEC, Ibrahim Aliyu Tunganwawa, yace za’a sake zaɓe a gundumomi biyu yau saboda wasu dalilai.
Jam’iyyar APC ta lashe kujerun ciyamomi a ƙananan hukumomi 25 dake faɗin jihar Neja a zaɓen da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (NSIEC) ta gudanar ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba, 2022.
Kwamishinan da ke kula da NSIEC, Ibrahim Aliyu Tunganwawa, shi ne ya sanar da Sakamakon a Minna, babban birnin jihar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Yace sabida wasu dalilai da suka taso, hukumar zaɓe zata canza zaɓe a wasu gundumomi biyu da ke kananan hukumomin Rafi da Kontagora.
Gundumonin biyu sun haɗa da Kusherki a ƙaramar hukumar Rafi da kuma Tungan a yankin Kontagora kuma an tsara gudanar da zaɓen yau.
Ibrahim Aliyu Tunganwawa, ya bayyana cewa zaɓen ya gudana cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali duk da an samu matsalolin da ba’a rasa ba.
Haka zalika, yace jam’iyyun siyasa 13 ne suka shiga suka gwabza a zaɓen ƙananan hukumomin.
PDP bata shiga zaɓen ba Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa babbar jam’iyyar hamayya PDP ta ƙauracewa zaɓen baki ɗaya, inda ta sanar da cewa zata ƙalubalanci matakan da ka bi wurin shirya zaben a gaban Kotu.
Bugu da ƙari, idan baku manta ba majalisar dokokin jihar Neja ta nuna adawa da shirin gudanar da zaɓen bisa hujjar Aljihun gwamnatin jiha ya rame ta yadda ba zai iya samar da isassun kuɗin da za’a yi zaɓen ba yanzu.
Hukumomi a Jihar Arewa A wani labarin kuma Kwankwaso, mai neman zama shugaban ƙasa yace APC da PDP sun tafka kuskuren wajen tsaida ɗan takara.
Yayin wata ziyara da ya kai jihar Ebonyi, Rabiu Kwankwaso yace jam’iyyar NNPP zata lashe zaɓen shugaban ƙasa cikin sauki saboda kuskuren jam’iyyu.
Tsohon gwamnan Kano ya kuma bayyana sunayen mutum biyu da ya so su lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyun APC da PDP.
Source:LEGITHAUSA