Ahmed Abubakar Audi, kwamanda janar na shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, NSCDC, ya ankarar da yan Najeriya kan bullar wata muguwar kungiya a kasar.
Audi, yayin jawabinsa wurin taron kwamandojin NSCDC a Abuja ya ce yan kungiyar suna saka kaya irin na jami’an tsaro sannan su rika tada hankalun mutane da kai hare-hare.
Shugaban na NSCDC ya zubarar da kwamandojinsu su dage wurin tattara bayanan sirri su kuma kare kayayyakin gwamnati da ke yankunansu musamman a halin yanzu da ake fuskantar zabe.
Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC), Ahmed Abubakar Audi, ya bayyana cewa akwai wata kungiya mai hatsarin gaske a Najeriya da ke haddasa rikici.
Audi ya bayyana hakan ne yayin bude taron kwamandojin rundunar na shekarar 2022 tare da kwamandojin jihohi a hedkwatar NSCDC a ranar Laraba a Abuja, Daily Trust ta rahoto.
Audi ya ce an gano kungiyar ne sakamakon bayanan sirri da hukumar ta samu, rahoton Blue Print.
Sabuwar Kungiya Mai Hatsari Ta Bullo, Suna Sanya Kayan Jami’an Tsaro –
Audi Shugaban na NSCDC yayin da ya ke zaburar da kwamandojin hukumar ya ce: “Akwai wata kungiya mai hatsari a gari. Mambobin na saka tufafi irin na jami’an tsaro kuma sun fara adabar al’umma.
“Don haka dole mu zage damtse mu gane wadannan mutanen.”
Ya zaburar da kwamandojin yankuna da jihohi su rika aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar sun kare kayan gwamnati a jihohinsu yayin da ke magana kan hare-haren da ake kaiwa INEC.
Shugaban NSCDC ya bukaci kwamandojin hukumar su kare kayayyakin INEC Audi ya ce: “Za mu tuhumi kwamandoji jihohi idan an kai hari a wata cibiyar INEC a jiharsu.”
Ya bukaci su mayar da hankali kan tattaro bayanan sirri, yana mai cewa ‘kare afkuwar laifi ya fi sauki fiye da magance shi’.
Shugaban na NSCDC ya bukaci kwamandojin yankuna su saka idanu kan tafiyar da jami’ansu, kuma zai rika sauraron bayanai na abin da ke tafiya a karkashin yankinsu duk minti-minti.
Ya bukaci su shirya tarukan kara wa juna ilimi ga jami’ansu don fadakar da su bukatan da ke akwai na biyayya ga dokokin zabe, musamman kamar yadda ya ke a sabuwar dokar zabe.