Kwamdan NSCDC na Abuja ya ce harin da yan ISWAP suka kaiwa gidan harin Kuje ba tare da turjiya ba ya kara basu karfin giwa na kara kaiwa wurea daban-daban hari a birnin.
Hukumar jami’an tsaro na jan kwala NSCDC ta gano shir-shiryen da kungiyar yan ta’addan ISWAP ke yi na yunkurin kaiwa wurare daban-daban hari a birnin tarayya Abuja.
Kwamandan NSCDC na FCT, Peter Maigari, wanda ya fitar da wannan rahoton a ranar Juma’a, 8 ga Yuli, 2022 wata lacca mai take; ‘Sabuwar Barazana Na Harin Da ‘Yan Ta’addar ISWAP ke yunkurin kaiwa FCT’, ya ce:
“Tabbatattun bayanan sirri sun nuna cewa mambobin kungiyar ta’addanci ISWAP, sun kammala shirin kaddamar da hare-hare a wasu zababbun wurare a cikin FCT kuma sun shelanta yaki da Kiristoci a Najeriya.”
Rahoton LEADERSHIP Wani kwafin rahoton jan kunne, da aka aika wa babban sakatare na hukumar babban birnin tarayya (FCTA) da LEADERSHIP ta gani ya ci gaba da cewa: “An samu karin bayanan sirri cewa kungiyar ta’adda ta ISWAP ta dauki alhakin harin da aka kai gidan yarin Kuje a ranar Talata, 5 ga Yuli, 2022.
Takardar bayanan da aka fitar ta yi gargadi akan harin baya-bayan nan da aka kai gidan yarin Kuje da ke Abuja, wanda ya dauki tsawon sa’o’i biyu ba tare da wata turjiya ba, ya nuna cewa a shirye suke da su kai hari a wasu wuraren tsaro, makarantu da cibiyoyin ibada a FCT, don haka suka saki membobinsu don cigaba da kai munanan hare-hare.”
Don haka Maigari ya bukaci a sake duba matakan tsaro da ake da su a babban birnin kasar domin dakile shirin ‘yan ta’adda.
Kungiyar Atiku Ta Nesanta Kanta Daga Rikicin PDP a jihar Ekiti Wata kungiya dake taya tsohon mataimakin shugabankasa Alhaji Atiku Abubakar yakin neman zaben a jam’iyyar PDP, a zaben mai zuwa, ta nesanta kanta da rikicin bangaranci da ya dabaibaye jam’iyyar a jihar Ekiti kamar yadda jaridar THIS DAY ta rawaito.
Kungiyar mai taken: ‘Atiku Mobilisers’ (TAM) ta yi nadamar yadda jam’iyyar PDP ta jihar ta kasu gida biyu, inda ta bukaci uwar jam’iyya karkashin jagorancin Dr. Iyorchia da su sa baki a cikin lamarin dan kawo karshen matsalar kamar yadda jaridar The SUN ta rawaito.