Hukumar NSCDC a Ilorin ta ce, ta cafke wasu maza uku da ake zargi da satar shanu shida da babur a yankin Gwanara na jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Babawale Afolabi, ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a a Ilorin, cewa rundunar ‘yan sanda ta ‘Agro Rangers’ ce ta yi kamun.
Ya kara da cewa, “an gabatar da shari’ar satar shanu shida ne ta hanyar wani dattijo mai shekaru 58 a duniya dake karamar hukumar Biogberu Baruten a ofishin NSCDC na Gwanara a ranar 26 Mayu, a kan wadanda ake zargi na kauyen Yere da Woru Sika Sebo da Jobo Gurukonna na kauyen Gbongbonru.”
“Har ila yau, karar fashin babur kirar Bajaj a ranar 17 ga Mayu, 2021, an gurfanar da ita a kan wadanda ake zargin. Wanda abin ya shafa ya yi korafin cewa bayanai sun same shi cewa wanda ake zargin tare da abokan aikinsa a cikin aikata laifi sun tafi da shanunsa guda biyar, bujimai da saniya daya a ranar 18 ga Mayu. Ya nemi taimakonmu don cafke wanda ake zargin da abokan aikinsa kuma daga karshe aka kame su,” in ji Afolabi.
Afolabi ya ce, “an samu nasarar kwato bindigogi biyu daga gida daga hannun wadanda ake zargin biyu kuma an gano babur din da ya bata daga Paraku a Jamhuriyar Benin.”
Ya kara da cewa, wasu mutane da ba a san su ba sun mayar da shanu biyar zuwa sansanin hukumar kuma wadanda ake zargin sun yarda su biya sauran ragowar shanun.
“Wannan yana tare ne da kudaden da mai korafi da mai shanun suka kashe kamar yadda ya nema da suka kai N400, 000,” in ji shi.
Afolabi ya kara da cewa, “haka kuma, kudin da mai ajaj din ya biya ya kai Naira 48,000.”