Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi a wajen kaddamar da kungiyar NRC ya bayyana cewa fulani fa ba yan ta’adda bane kamar yadda wasu suke yi musu kallo a Najariya
Gumi ya bayyana hakan ne cikin. jawabin da ya yi a madadin Farfesa Umar Labdo yayin kaddamar da kungiyar kare hakkin makiyaya, NRC.
An kafa kungiyar ne da nufin kare hakkin dukkan makiyaya ta hanyar amfani da doka ba tare da banbancin kabila, addini ko yanki ba.
Shugaban Kungiyar Kare Hakkin Makiyaya ta Nomadic Rights Concern (NRC), Farfesa Umar Labdo, ya ce fulani ba yan ta’adda bane, ko yan fashi ko bata gari, Nigerian Tribune ta rahoto.
A yayin taron manema labarai da ta kira a Kaduna a ranar Alhamis, yayin kaddamar da kungiyar, Labdo ta ce lokaci ya yi da yan Najeriya za su san cewa akwai bata gari a kowanne kabila. Don haka babu dalilin da zai sa a rika alakanta fulani da fashi ko ta’addanci.
Shugaban na NRC, wanda ya samu wakilcin Dr Ahmed Gumi, ya ce: “An kafa kungiyar ne don cike gibin da ke tsakanin sauran al’umma da makiyaya.
Duba da rikicin baya-bayan nan da ya shafi makiyaya, abin da ke akwai shine ana daukan makiyaya a matsayin masu aikata laifi da wanda ake yi wa laifin saboda karancin ilimi.”
A cewarsa, “wannan kungiyar za ta bi kadin hakokin Fulani da ake take wa ko hana su, hakan ke haifar da abubuwa da dama bai kamata su faru ba.
“Rikici ba abin alheri bane. Don haka ya zama dole a kafa kungiyar da ba na gwamnati na kuma ba na siyasa ba don samar da zaman lafiya tsakanin kungiyoyi da kabilai, musamman makiyaya da manoma.”
“Kungiyar ta ce babban manufarta shine kare makiyaya a Najeriya da wasu kasashen ta hanyar amfani da kotu da kundin tsarin mulkin kasa.
“NRC za ta yi hadin gwiwa da dukkan kungiyoyin Fulani don tabbatar da hadin kai tsakaninsu. “Wannan kungiyar ba na Fulani ne kadai ba, na dukkan makiyaya ne ko daga wace kabila da yanki da addini.”
A cewarsa, kungiyar ta kare hakkin makiyayan za ta rika amfani da hanyoyin zamani na kimiyya wurin kiwon dabobi da inganta harkar baki daya.
Tsaro: Sheikh Gumi Ya Gargadi Jami’an Tsaro Kan Kama Matasan Fulani Barkatai Da Sunan Yaki Da Yan Bindiga.
A wani rahoton, Sheikh Ahmad Gumi, ya gargadi hukumomin tsaro game da kama matasan fulani barkatai da suna yaki da ta’addanci, rahoton Daily Trust.
Da ya ke magana a wurin taron kaddamar da Kungiyar Kare Hakkin Makiyaya a Kaduna, Sheikh din ya ce kawo yanzu, akwai matasan fulani da yara da yawa a wadanda ba su ji ba ba su gani ba a tsare.
Ya ce dalilin kafa kungiyar shine tabbatar da cewa matasan Fulani da ba su aikata komai ba sun samu adalci, ya kara da cewa za ta taimaka wurin kawo zaman lafiya a kasar.