Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars tayi rashin nasara a hannun Akwa United da ci 3-0 a gasar firimiya ta kasa NPFL ta kakar wasannin shekarar 2021/2022.
Wasan dai ya gudana da yammacin ranar Lahadi 19 ga Disambar 2021 a garin Uyo da ke jihar Akwa Ibom.
Dan wasan Ezekiel Bassey ne ya fara zura kwallon farko tin kafin zuwa hutun rabin lokaci bayan tai mako da ya samu daga hannun Stephen Chukwude.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne dan wasa
Ubong Friday ya kara kwallo ta biyu a minti na 52.
Kana dan wasa Friday ya sake zura kwallo ta ukun bayan samun tai mako daga hannun John Lazarus.
Wasan dai shine mako na farko na sabuwar kakar wasannin shekarar 2021/2022.
A kakar wasannin data gaba dai kungiyar kwallon kafa ta Akwa United ce ta lashe gasar ta NPFL, inda a yanzu ta ke kare gasar da ta lashe inda ta samu nasara a wasan farko data buga.
Sauran sakamakon wasannin da aka buga a mako na farko sun hada da
Akwa United 3- 0 Kano Pillars
Enyimba 2-1 Abia Warriors
Katsina Utd 1-2 Rangers
Gombe Utd 0-0 3SC
Heartland 3-3 Nasarawa United
Nijer Tornadoes 1-0 Plateau United
Lobi Stars 1-1 Rivers United
Kwara Utd 3-1 Dakkada
MFM FC 0-2 Remo Stars