An bayyana cewa yanzu haka Nijeriya ce ta daya wajan yawan noma Gero, da samar da miliyoyin Tan Tan na Gero a Nijeriya wanda kuma anfi noma shine a yammacin afirika wanda jamhoriyyar nijar ke da fadin kasa na noma Gero kuma Nijeriya ta fita samar da Gero mai yawa a wannan lokaci.
Haka kuma Nijeriya ce ta uku wajan noma Gyada a duniya, ta hanyar samar da tan sama da miliyan hudu kamar yadda bayanai su ka tabbatar da haka a shekarar 2021 na yawan noma gyada a Nijeriya wacce it ace ta uku a duniya inda kasar Amerika ta ke ta daya a noma gyada a duniya a yayin da kasar Ustireliya ta ke a matsayin ta biyu wajan samar da gyada a duniya.
Wannan bayanin ya futo ne daga bakin mataimakin shugaban sashin nazarin noma na DLA da ke Jami`ar Bayero da ke kano Farfesa Muhammad Sunusi Ahmad Gaya a lokacin ya ke yiwa manema labarai karin haske a wajan taron nazarin samar da ingantaccan irin shuka da aka yi taron kasa da kasa wanda ya hada da daukacin masu ruwa da tsaki kan bunkasa noma kamar Masana, manoma, `yan kasuwa da masu sarrafa kayan amfanin Gona wanda taron kasa da kasan ya gudana a birnin kano a ranar Alhamis da ta gabata.
Har ila yau Farfesa Gaya ya ce ganin yadda ake fama da matsaloli a bangaran shuka yasa a ka shirya wannan taro na kasa da kasa inda wakilan kasashin irin su Ustireliya, Mali, Kenya, Birkina Faso da Kuma Nijeriya duk su ka samu wakilci a wannan taro da nufin lalubo hanyoyin warware matsaloli akan irin shuka musamman akan irin Gero, Dawa, Wake, Gyada wanda kusan su ne akafi dogara da su a wannan yanki na mu na Afirika har ma da kokarin samar da irin wanda zai da ce da ko wanna yanayi na dumamar yanayi da duniya ke fuskanta a yau a cewar gaya.
A karshe dai ya yi kira da manoma da sauran masu ruwa da tsaki kan a rika tuntubar masana akan ko wacce matsala akan harkar noma haka kuma masana surika tuntubar manoma da sauran masu ruwa da tsaki a kan duk kan wani abu da ya shafi buncike domin masu ruwa da tsaki ne suka san abunda ya kamata a bunciko musu, ka da masana su tsaya su ka dai a makarantu da cibiyoyi wajan bunkice ba tare da masu ruwa da tsaki ba a Nijeriya.