Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) ya sanar da shirin fara hakar man fetur a Jihar Nassarawa a cikin watan Maris mai zuwa wanda ke matsayin karon farko da aka gano irin wannan albarkatu a jihar ta Arewacin kasar nan.
Matakin gano rijiyar man a Nasarawa dai na zuwa ne a wani yunkuri da NNPC ke yi don lalubo sauran sassan kasar nan da ke da irin wannan albarkatun karkashin kasa a cikin Nijeriya.
NNPC karkashin jagoranci Mele Kyari, na ci gaba da baza koma don lalubo man fetur a kan tsaudari sabanin cikin ruwa da a baya kasar nan ke lalube a yankin kudanci.
Lokacin da ya ke karbar bakoncin tawagar wakilcin al’ummar ta Jihar Nasarawa karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Sule a hedikwatar kamfanin na NNPC da ke Abuja, Kyari ya bayar da tabbacin cewa kamfanin zai jagoranci aikin hakar man cikin watan Maris mai zuwa.
A watan Nuwamban bara ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hakar man fetur a jihohin Bauchi da Gombe shekaru biyu bayan sanar da gano albarkatun man a jihohin biyu na Arewacin Nijeriya irinsa na farko a tarihin kasar nan.
A wani labarin na daban mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin.
Ya ce Sin na kira ga kasashen Amurka da Japan, da su kauracewa tunanin cacar-baka, da akidun nuna wariya, su kuma dakatar da kirkirar wasu makiya na jabu, da rura wutar yakin cacar-baka a yankin Asiya da Fasifik, kana bai dace su kasance masu gurgunta yanayin daidaito da ake da shi a yankin Asiya da tekun Fasifik ba.
Wang Wenbin, wanda ya yi wannan tsokaci a jiya Jumma’a, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa, game da sanarwar hadin gwiwar kasashen biyu, ya ce rahotanni sun tabbatar da cewa, cikin waccan sanarwa ta Amurka da Japan, kasashen 2 sun kira Sin “Babbar kalubale a yankin tekunan Indiya da Fasifik, da ma karin wasu yankunan”.
Sanarwar ta kuma soki kasar Sin, don gane da manufofin ta game da yankin Taiwan, da Hong Kong, da jihar Xinjiang, da ma manufofin kasar masu nasaba da teku.
Wang, ya ce Amurka da Japan, na cewa suna tallafawa zaman lafiya da tsaron shiyyoyi, amma a zahiri suna lalubo hanyoyi ne na gina tsarin girkewa, da amfani da karfin soji.
Kaza lika suna cewa burin su shi ne samar da yanayin gudanar da harkoki a bude, a yankin tekunan Indiya da Fasifik, amma kuma abun da suke yi shi ne, kafa tsarin rarraba kawuna, da haifar da fito na fito. (Saminu Alhassan)
Source:LegitHausang