Daraktan ma’aikatar man fetur ta kasa (NNPC) Mele Kyari, ya bayyanawa manema labarai cewa, shigo da man fetur daga kasashen ketare zai zo karhe a Najeriya a tsakiyar shekarar 2023.
Kyari yana wannan jawabin ne yayin da yake amsa tam,bayoyin manema labarai a gidan gwamnati ranar talata 30 ga watan august 2020.
A cewar gamayyar matatun man fetur din Najeriya wadanda aka yima garanbawul da kuma matatun man fetur dain da Dangote yake dasu sun isa wadatar da Najeriya kuma saboda wannan dalili za’a daina shigo da man fetur din.
”Saboda haka baku da bukatar shigo da man fetur daga kasashen ketare ba zuwa tsakiyar shekara” kamar yadda ya bayyana.
Shugaban NNPC yace duba da cewa gwamnati ta mallaki kashi 20 cikin dari na matatun man fetur ta bangaren Dangote abu ne mai sauki ta ce ta daina shigo da man fetur din daga kasashen waje.
Kamar yadda ya bayyana matatar tana da ikon samar da ganga 650,000 a rana daya sakamakon sabuwar fasaha da aka samu.
Shugaban NNPC yace yana fatan Najeriya ta wata babbar cibiya ta samar da ma’adanan man fetur da sauran su ba wai a Afirka ta yamma kadai ba har ma a duniya baki daya.
Yace yana da tabbacin zuwa tsakiyar shekarar 2023 yanayin fitar da man fetur daga Najeriya zai canja sosai da sosan gaske.
Najeriya na cikin kasashe masu arzikin ma’adanai ciki har da man fetur amma sai dai tattare da hakan kaso mafi yawa na man fetur din da ake amfani dashi a kasar ana shigo dashi ne daga kasashen ketare wanda hakan ya sanya man fetur yayi kazamar tsada a kasar.
Idan masu amfani da man fetur zasu same shi cikin sauki ba tare da an shigo dashi daga wani waje ba abubuwa da dama zasuyi sauki kuma za’a samu saukin rayuwa, kamar yadda wani masanin tattalin arziki ya tabbatar mana