Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban rikon kwarya na hukumar cigaban yankin Neja Delta, watau Niger Delta Development Commission (NDDC), Effiong Akwa.
Har yanzu ba’a bayyana takamamman dalilin cire Effiong ba, riwayar TheNation.
Diraktan yada labarai na ma’aikatar lamuran Neja-Delta (NNDC), Patricia Deworitshe, a bayyana hakan a jawabin da ya fitar.
Ya bayyana cewa Shugaban kasa zai kafa sabuwar kwamitin shugabannin hukumar kuma za’a sanar da sunayensu daga baya.
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta saki sabbin sunaye na ‘ya’yan kwamitin yakin neman zabenta na shugaban kasa.
A wannan karon ma wasu jaruman masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood sun samu shiga jerin.
Sai dai kuma, ko sama ko kasa ba a ga sunan shahararran mawaki Daudu Kahutu Rarara ba wanda a da yana cikin kwamitin.
A wani labarin na daban Jam’iyyar APC ta saki sabbin sunaye na mambobin kwamitin yakin neman zaben dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bayan ta yi yan gyare-gyare a wanda ta fitar a baya.
Har yanzu shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma’ila Na’abba Afakalla na nan a matsayin mataimakin darakta a bangaren masu nishadantarwa na kwamitin kuma zai jagorancin yankin arewa maso yamma.
Jarumi Nuhu Abdullahi na nan a matsayinsa na mataimakin mai kula da jin dadin kwamitin yan wasan.
Sani Idris Moda ma yana nan a cikin kwamitin.
Sai dai kuma, a wannan karon, ba a ga sunan shahararren mawakin siyasa, Daudu Kahutu Rarara ba a cikin wanda a da shine ke rike da mukamin jami’in kula da harkokin kwamitin na yan wasa.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Rarara ya saki sabuwar waka inda ya soki Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano.
A cikin sabuwar wakar da ya fitar don yi wa Tinubu kamfen, Rarara ya tabbatar da rikicinsa da Ganduje kuma ya bayyana gwamnan a matsayin ‘Hankaka’, ma’ana mutum mai fuska biyu.
Rarara kuma ya zargi Ganduje da daƙile saka sunansa a kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC.
A wani labarin, wata kungiyar goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mai suna Jagaban National Coalition ta fara bi gida-gida tana yi masa kamfen.
Jagoran kungiyar a jihar Plateau, Mista Zakariyau Adigun, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a garin Jos, a ranar Talata, 18 ga watan Oktoba.
Adigun ya ce shirin kungiyar shine sanar da duk wani dan jihar nasarorin Tinubu da kyawawan shirin da yake yiwa kasar, rahoton Vanguard.
Source:legithausang