Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) a Jihar Kebbi, ta yi kira ga gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu, da ya aiwatar da tsarin daidaita albashin ma’aikata mafi karancin na N30,000 ga ma’aikatan jihar.
Shugaban kungiyar na jihar, Kwamared Murtala Usman, ne ya yi kiran a yayin jawabinsa na ranar bikin ma’aikata na bana a masaukin shugaban kasa da ke a Birnin Kebbi, ya ce bikin zagayowar ranar ma’aikata ita ce mai taken “Aiki mai fa’ida ga mata da maza a cikin yanayi na ‘yanci, daidaito, tsaro da mutuncin dan Adam”, a zahiri, ana daukar aiki da kyau idan: ana biyan ma’aikata kudaden albashi a kan gaskiya.
Ya kara da cewa an ba da tabbacin aiki kuma akwai yanayin aiki lafiya; akwai daidaitattun dama da magani ga kowa; akwai kariyar zamantakewa ga ma’aikata da kuma iyalansu; akwai tsammanin ma’aikata don habaka kansu da kuma idan yana karfafa hafin gwiwar zamantakewa; ana barin ma’aikata cikin ‘yanci don bayyana damuwarsu kuma su tsara. Dangane da bayanan da ke sama muna da bukatu kamar haka: daidaitawa tsarin fansho kashi uku da muke da shi wanda ya kasance 12%, 15.5% da 33% da aiwatar da kashi 30% daidaitaccen sakamako.
Haka kuma ya ce, kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma a jihar na fatan gabatar da bukatarsu don yin la’akari da yiwuwar aiwatar da su Alawus alawus ga duk ma’aikatan jinya da ungozoma a fadin jihar, cikakkun aiwatar da tsarin albashin CONHESS, inganta tsaro don bai wa ma’aikatan jinya da ungozoma damar gudanar da ayyukansu na doka musamman a yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro, sai dai daidaita albashi ga malamai a kwalejin kimiyyar jinya da sauran batutuwa.
A cewar shugaban, akwai bukatar a yi la’akari da yadda ake gudanar da nade-naden mukamai a ma’aikatar jihar, kamar shugaban ma’aikatan gwamnati, sakatarorin dindindin da sauran wadanda suka dade su na rike da mukamai na rikon kwarya. Hakazalika da daidaita nade-naden nasu zuwa manyan mukamai zai taimaka matuka wajen inganta ayyukan ma’aikatan Jihar Kebbi.
Shugaban kungiyar NLC, ya yi nuni da cewa, taken ranar Ma’aikata na shekara ta 2023 wanda shi ne “Hakkin ma’aikata da adalci na zamantakewar al’umma” na da shakku ganin yadda ake tauye hakkin ma’aikata a wuraren aiki da kuma a jihohi da dama a fadin kasar nan. Yana da kyau a lura da cewa tauye hakkin ma’aikata na iya haifar da hana musu adalci na zamantakewa da tattalin arziki, a wurare da yawa na aiki, mahimman abubuwan da ke da mahimmanci don samun kyakkyawan aiki, wanda yana daya daga cikin hakkin ma’aikata masu aiki ba su bayar ba.
Daga bisa sun mika godiya da jinjina wa gwamna Abubakar Atiku Bagudu bisa biyan kudin gratuti da kuma cikin hakkin ma’aikatan Jihar Kebbi
A nasa jawabin, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, ya ce “Na lura da dukkan bukatar da shugaban Kwadago na jiha, Kwamared Murtala Usman ya gabatar da kuma kiran da ake yi na a rika nada mukamai zuwa kwakkwaran aiki.’
Ya kuma ba da tabbacin ga ma’aikata don yin la’akari da aiwatar da su. Haka kuma Gwamnan ya yi karin bayani kan biyan kashi 40% na kwanan nan da gwamnatin tarayya ta amince da shi ga ma’aikata a matakin tarayya, ya kamata kungiyar kwadago ta fahimci cewa ba karin albashi ba ne don kaucewa haifar da wata muhawara tsakanin su da gwamnati a nan gaba kadan.
Gwamnan, ya kara da cewa amincewar ta kasance don daidaita albashin ma’aikata don daidaitawa da ma’aikatan da aka bar su a baya na ma’auni guda.
Ya kuma shawarci shugabannin kungiyar da su fara tunanin mafita da yadda za su jagoranci muhawara kan batun tallafin man fetur, domin nan ba da jimawa ba gwamnatinmu ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin man fetur ba saboda muna fatara da tallafin mai a kasar nan, inji shi.
Bugudu, ya bayyana jin dadinsa da kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da daukacin kungiyar kwadago a jihar, inda ya bukace su da su yi irin wannan aikin ga gwamnati mai zuwa, yayin da ya ce “Na biya kungiyar kwadagon bisa ga goyon bayan da na bayar ga wani mamban na tabbatar da cewa na tsayar da shi dan takarar gwamna don ya gaje ni, ya kuma lashe zabe yanzu shi ne wanda zai gade ni”.
Source:LeadershipHausa