Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara da ya sake sabunta albashin ma’aikata don kara albashin zuwa kashi 50 cikin 100, idan aka yi la’akari da yadda rayuwa take tafiya a kasar nan.
Ta bayar da wannan shawarar ce a cikin wasikar da shugaban NLC na kasa Ayuba Wabba ya rattaba wa hannu ya kuma tura wa Buhari.
Daukacin Gwamnoni Za Mu Hada Kai Don Share Wa NLC Hawaye – Gwamna Ganduje
Wasikar mai dauke da kwanan wata 8 ga watan Agustan 2022, kungiyar ta bayar da wannan shawarar ce biyo bayan shawarar da kungiyar gwamnonin kasar ta bai wa Buhari na yiwa ma’aikatan da suka haura shekaru 50 ritiya daga aiki.
Kungiyar wacce ta soki gwamnonin kan wannan sahawara ta su, ta sanar da cewa, maimakon a yiwa ma’aikatan ritaya, kamata ya yi ace gwamnatin ta kara musu albashi.
NLC ta kuma jinjina wa shugaba Buhari kan karin albashi mafi karanci na ma’aikatan gwamtin tarayya.
A wani labarin na daban Shugaban karamar hukumar Kankara da ke Jihar Katsina ya yi kira al’umma su ci gaba da gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Alhaji Anas ya yi wannan kiran ne a lokacin taro a kan sha’anin tsaro wanda ya gudana a karamar hukumar Kankara.
Shugaban karamar hukumar ya ce an tattauna a kan hanyoyin da za a bi don inganta sha’anin tsaro a karamar hukumar.
Ya kara da cewa taron ya kuma fito da wasu dabaru wadanda za a bi domin maganace matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin.
Ya jaddada cewa kokarin da gwamnatin jiha ta yi ya taimaka wajen sake bude hanyar Birji wadda ta tashi daga Kankara zuwa Malali ta isa Zango ta karasa Dansabau bayan an rufe ta shekaru 3 da suka wuce sakamakon ayyukan ‘yan bindiga.
Alhaji Anas ya yaba wa sarakunan gargajiya, jami’an tsaro da mambobin kungiyar sa-kai wajen inganta sha’anin tsaro a yankin
Source: Leadership