Shugabancin kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) da (TUC) sun sanar da fara shirin yajin aikin gama gari a fadin kasar nan a ranar Talata mai zuwa 14 ga watan Nuwamba 2023.
Shugabannin kungiyoyin biyu sun cimma wannan matsaya ne bayan wani taron majalisar zartarwa ta kasa da suka yi a ranar Talata a Abuja.
Manyan kungiyoyin kwadagon biyu sun ce an fara hadar-hada mambobi da abokan hulda a fadin kasar nan take.
Matakin da kungiyar kwadagon ta dauka ya biyo bayan cin zarafin da aka yi wa shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero a makon jiya a jihar Imo.
An dai yi ta cece-kuce inda aka zargi kwamishinan ‘yansandan jihar Imo Mohammed Barde da hannu a harin da aka kai Ajaero a Owerri, babban birnin jihar Imo.
Kungiyar Kwadago a ranar Juma’ar da ta gabata ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki biyar domin ta maye gurbin kwamishinan ‘yansandan, yayin da ta kuma zargi Gwamna Hope Uzodimma da ke neman a sake zabensa da hannu a harin da aka kai wa Ajaero duk da cewa Gwamnan ya ce ba shi da hannu a harin.
Kungiyar Kwadago ta kuma bukaci a kama tare da gurfanar da wasu daga cikin hadiman gwamnan tare da yin barazanar daukar wani mataki na masana’antu a fadin kasar nan idan ba a aiwatar da bukatunsu ba.
Tuni dai, Sufeto Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, ya sauya wa Barde wurin aiki gabanin zaben gwamnan jihar Imo da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Source LEADERSHIPHAUSA