Karatun zamani na Nijeriya ya sami ci gaba tare da horar da matasa ‘yan Nijeriya 178 a cikin shirin da aka kammala kwanaki 10 na Stem Bootcamp for Kids (SB4Kids). da taimakon NITDA
Ya ce horon ya karfafa mahalarta taron da basu asalin makaman ilimin fasaha a aikace daidai da Manufofin Tattalin Arzikin kasa (NDEPS) na Gwamnatin Tarayya.
Kashifu ya ce hukumar NITDA ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa da karfafawa matasa masu kirkirar fasaha a Nijeriya.
Ya bayyana cewa akwai bukatar sabbin dabaru don ilmantar da tsarin STEM cikin tsarin ilimin na Kasa.
Ya ba da shawarar gabatar da fasaha mai gudanar da kanta (AI Robotics), Ayyukan yanar gizo-gizo (IoT), da sauran fasahohin da ke tasowa cikin manhajar.
Wannan wani babban kokari ne da hukumar ta samar kuma abin a yaba ne.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran Mawazin News ya bayar da rahoton cewa, an fara daukar tsauraran matakan tsaro a kasar Iraki domin tarukan arba’in da za a gudanar.
Rahoton ya ce, a yankin Bagdad jami’an tsaro suna sintiri a cikin gari da kuma cikin dazuzzuka domin tabbatar da cewa babu wasu ‘yan ta’adda da za su kawo barazana ta tsaroa yayin gudanar da tarukan Arba’in.
Baya ga haka kuam sauran yankuna musammanma biranan Karbala da kuma Najaf, tun bayan kammala taruka ashura har yanzu jami’an tsaro suna nan cikin shirin ko ta kwana.
Daga cikin matakan da ake dauka dai kula da layuka na wutar lantarki da kuma layukan butun gas, kamar yadda kuam ake sanya ido a kan dukkanin kai koma na jama’a.
Sannan kuma an kafa kamarori masu daukar hotunan bidiyo a dukkanin yankuna da titina na mayna birane musamman Karbala da Najaf.