Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), Caroline Wuraola Adepoju, ta ce hukumar za ta sayi kananan jiragen sama da jirage masu saukar Angulu da kuma jirage masu sarrafa kansu wato don gudanar da sintirin tsaro a iyakokin kasar nan.
Caroline ta ce hakan zai taimaka wa hukumar wajen sauke nauyin da aka dora mata, musamman wajen sa ido akan zirga-jirgar jama’a na shige da fice a iyakokin kasar, har a ta hanyar ruwa.
Ta bayyana hakan a Legas a taron bita da hukumar ta shirya a rundunar hukumar da ke filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke a jihar.
Kazalika ta ce, wadannan kayan aikin da za a siya, tuni an sanya su a cikin kasafin kudi na 2024 na ma’aikarar kula da harkokin cikin gida.
Bugu da kari, baya ga sayen wadannan kayan aikin, ta ce hukumar na kuma kan ci gaba da zuba jari a fannin kimiyya domin sarrafa takardun tafiye-tafiya da kuma sauran tsare-tsare don kara bunkasa tsaro a iyakokin Nijeriya.
A cewarta, daga shekara mai zuwa, hukumar za ta tura kofofi masu aikin da wutar lantarki a filayen jiragen sama na kasar don a sauwake wa fasinjoji shiga da fita daga cikin kasar.
Bugu da kari ta yi nuni da cewa, wannan ya nuna kokarin da ministan kula da harkokin cikin gida Dakta Olubunmi Tunji Ojo ke yi akan ajandarsa ta kara tabbatar da tsaro a iyakokin Nijeriya.
A na sa jawabin, Mista Fela Durotoye sabon babban mai taimaka wa na musamman ga shugaban kasa akan darajar kasa da yin adalci, ya shawarci hukumomin da ke aiki a filin jirgin da su hada hannu don su samar da bayanan sirri akan kokarin fa kasar ke yi, na bunkasa tattalin arzikin kasar.
Ita kuwa Kwantirolar rundunar ta filin jirgin uwargida Adeola Adesokan ta bayyana cewa, hada karfe da karfe a tsakanin jami’an tsaro da mahukuntan da ke sa ido a iyakokin kasar, hakan ya kara taimaka wa wajen samun karin masu zuba jari a cikin tattalin arzikin Nijeriya.
Kazalika, Manajin Darakta na hukumar jiragen sama ta kasa Kabir Yusuf ya bayyana cewa, hada karfi da karfe a tsakanin hukumomin na ci gaba da amfanarsu.
Source LEADERSHIPHAUSA