Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta sake jaddada kira ga kafafen yada labarai su rubanya kwazonsu wajen bayar da rahotannin da suka kamata a kan tafiye-tafiyen kasashen waje ta barauniyar hanya da kuma fadakar da jama’a game da hadarin da ke tattare da hakan.
Hukumar ta yi kiran ne a yayin gudanar da wani taron wayar da kai ga ‘yan jaridu da ya gudana a Abuja a ranar Litinin, a otel din Reiz Continental.
Shugaban Hukumar, CGI Isah Idris Jere ya yi kiran ta bakin wakiliyarsa a taron, Babbar Jami’a Mai Kula da Sashen Tafiye-tafiye a shalkwatar hukumar, ACG Ngozi Odikpo. Wakiliyar ta gabatar da Makala a kan abubuwan da ya kamata ‘yan jarida su mayar da hankali a kai wajen bayar da rahotanninsu game da yadda jama’a ke kaura ta hanyar da ta dace da kuma masu bin barauniyar hanya, tana mai jaddada cewa, ya kamata kafafen yada labarai su rika hadawa da labarun mutanen da suka fada komar masu safarar bil’adama ba bisa ka’ida ba domin wayar da kan al’umma a kan mummunan hadarin da ke tattare da hakan.
Har ila yau, tsohon shugaban hukumar ta NIS, Muhammad Babandede wanda ya yi jawabi a kan batutuwan da suka shafi tafiye-tafiye da suka halasta da wadanda suka haramta, da kuma su kansu mutanen da ke tafiye-tafiyen, ya nuna akwai bukatar kafafen yada labarai su rika bayar da rahotannin da suka dace na kiyaye mutuncin Nijeriya, yana mai ba da misali da irin kalaman da ake amfani da su wajen bayar da rahotannin da suka shafi kasa domin wayar da kan ‘yan kasa.
Ya nemi a rika fada wa ‘yan kasa gaskiyar abin da yake faruwa ta hanyar ilmantarwa da kuma fadakar da su game da tafiye-tafiye da ke kan ka’ida da kuma wadanda suka saba.
Kungiyar ‘Yan Jarida Masu Rubuta Labarun Tafiye-tafiyen Kasashen Waje ta Duniya (JIFORM) tare da hadin gwiwar Cibiyar Kula da Tafiye-tafiye ta Kasar Jamus (NGC) suka shirya taron a kan yadda za a inganta bayar da rahotannin da suka shafi tafiye-tafiye ba bisa ka’ida ba da hadarin hakan.
Wakazalika, Kwanturolan NIS na Jihar Ribas, CI James Sunday ya gabatar da makaloli biyu a wurin taron domin wayar da kan ‘yan jarida a kan hakkokin da suka rataya a wuyarsu na bayar da rahotannin tafiye-tafiyen da suka dace da wadanda suka saba wa doka.
Taron ya kuma samu halartar manyan baki daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sauran kungiyoyi masu nasaba da kai-komon jama’a.