Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), ta tabbatar da cewa ta bi ƙa’ida sau da ƙafa wajen bayar da Fasfon Nijeriya ga ɗan samarin nan, Mista David Ukpo Nwamina da ake ƙiƙi-ƙaƙa a kansa game da batun cire wata gava a jikinsa domin dasa wa wata yarinya mara lafiya, ‘yar gidan tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu.
Wata sanarwar manema labarai da Shugaban NIS, CGI Isah Idris Jere ya fitar tare da rattaba hannu da kansa, ta yi bayanin cewa yamaɗiɗin da wasu ke yaɗawa, “cewa hukumar ba ta tantance takardun wanda aka bai wa fasfon yadda ya kamata ba, ba gaskiya ba ne illa ƙazafi da wasu suka kitsa don kawai su shafa wa hukumar kashin kaji a vata mata suna.
“Don haka gaskiyar abin da ya faru game da lamarin shi ne, shi wanda ake magana a kansa, Mista David Ukpo Nwamina ya gabatar da buƙatarsa ta sabon fasfo da aka inganta kuma ya biya kuɗin fasfon ta manhajar intanet wanda bayan haka ne ya tafi Ofishin Fasfo na Abuja da ke Gwagwalada a ranar 2 ga Nuwambar 2021 domin amsa tambayoyi.
Domin ƙarfafa samun fasfon nasa, Mista David Nwamina ya gabatar da dukkan takardun ƙa’ida da suka wajaba, da suka haɗa da takardar haihuwarsa wadda Hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) ta ba shi, da ta nuna an haife shi a ranar 12 ga Oktobar 2000, sannan bayanan shaidar haihuwarsa ta lambar ɗan ƙasa wadda Hukumar NIMC ta ba shi, sun yi daidai da na takardar haihuwarsa sai kuma takardar shaidar asalinsa wadda Ofishin Gwamnatin Jihar Ebonyi na Abuja ya ba shi da kuma takardar shaidar mutumin da ya tsaya masa da aka rattaba wa hannu kamar yadda ya kamata.”
Saboda haka bisa waɗannan hujjoji, NIS tace tana sanar da jama’a cewa ba ta wallafa ranar haihuwa ko wasu bayanai a duk wani fasfon Nijeriya har sai an tantance su yadda ya kamata tare da tantance shi kansa mai neman fasfo. “Don haka batun Mista Nwamina ba zai zama daban ko na ɗanmowa ba.”
Har ila yau, Hukumar ta NIS ta tabbatar wa da al’umma irin duƙufar da ta yi wajen kare mutuncin fasfon Nijeriya, kana ta yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga jama’a su guji furta irin waɗannan ƙarairayi domin za su iya zubar da kimar hukumar a idon duniya.
Mista David Ukpo Nwamina dai na can Ingila ana ci gaba da bincike a kansa da wanda abin ya shafa Sanata Ike Ekweremadu.