A ranar Larabar da ta gabata ne wasu masu hulda da kamfanonin sadarwa suka nuna rashin jin dadinsu kan katse layinsu da kamfanonin sadarwa suka yi daga tsarin kiran waya, duk da cewa kuwa, sun bi umarnin alakanta lambarsu ta kasa (NIN) da layinsu na kiran waya (SIM).
Masu hulda da kamfanonin sun bayyana rashin jin dadin su ne a wata hira da suka yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, NAN a Legas.
NAN ta ruwaito cewa, kamfanonin sadarwa a Nijeriya da suka hada da MTN, Airtel, da Globacom da dai sauransu, hukumar kula da harkokin sadarwa ta Nijeriya, NCC ta basu umurnin aiwatar da cikakkiyar dokar katse layi daga tsarin kiran waya ga duk wani layin da ba a alakanta shi da NIN ba ko kuma wadanda sun alakanta amma ba a iya tantance NIN din ba zuwa 28 ga watan Fabrairu, 2024.
A wani labarin na daban wata kungiyar kudancin Nijeriya mai zakulo manyan masu tasiri a kafafen sada zumunta a duk shekara mai suna TheJoY150.
Ta zayyana sunayen jarumin fina finan Hausa Ali Nuhu da kuma Murja Ibrahim Kunya a cikin jerin mutane 150 da suka fi tasiri ko suka fi bayar da nishadi a cikin shekarar 2023 da ta gabata.
Daga cikin yan arewacin Nijeriya da suka samu shiga wannan jadawali akwai.
Ali Nuhu, Murja Kunya, Nasiruddin Abdulmumin, Rahama Sadau, Ireti Kingibe, Abdallah Uba Adamu, Auwal Musa Rafsanjani, Natasha Akpoti da kuma Bishop Matheu Hassan Kukah.
A duk shekara kungiyar takan zakulo manyan mutane wadanda take ganin sunfi bayar da gudunmawa a kafofin sada zumunta ta hanyar Nishadantarwa ko Ilimantarwa.
Source: LEADERSHIPHAUSA