Nijeriya ta bai wa Amurka mamaki da ci 90-87 a wasan sada zumunta na kwallon kwando na shirye shiryen zuwa gasa Olympic, wasan da aka fafata a birnin Las Vegas, Nevada a ranar Asabar.
Nijeriya, wadda ke da ‘yan wasa 6 da ke fafatawa a gasar NBA ta Amurka, da kuma kocinta Mike Broewn, wanda tsohon dan wasan NBA ne ta kasance kasar Afirka ta farko da ta taba doke Amurka.
Tawagar Amurka ta yi wasan ne ba tare da ‘yan wasanta 3 da ke kan ganiyarsu ba.
shahararren dan wasan Brooklyn Nets Kevin Durant ne ya sanya Amurka a gaba da maki 17.
Nasarar da Nijeriya ta samu ta zo ne shekaru 9 bayan Amurka ta lallasa 156-73 a gasar Olympic da aka yi a birnin Landan.