Nijeriya IMN Ta Nuna Damuwarta Da Hana Sheikh Zakzaky Da Matarsa Passport Nasu.
A cikin wani bayani wanda sakataren “Academic Forum” na kungiyar IMN ko harkar musulunci a tarayyar Najeriya ya fitar a jiya Umma’a, kungiyar ta bayyana damuwarta da ci gaba da hana shugaban Kungiyar Sheikh Ibrahim Zakzaky da kuma Matarsa Malama Zinat Passport Nasu, don neman magaji a kasashen waje.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce ta sami kofin bayanin wanda Engineer Abdullahi Musa ya sanyawa hannu. In ya yi bayanin cewa ‘Duk tare da nasarorin da Malam da Matarsa suka samu a gaban kotu a cikin ‘yan watannin da suka gabata gwamnatin tarayyar kasar ta ci gaba da hana su fita daga kasar don neman magani, saboda hanasu passport nasu’.
Musa ya kara da cewa: Har yanzu malam da matarsa suna fama da raunuka masu yawa a jikunansu, raunuka wadanda suke barazana ga rayuwar su idan basu sami ganin likitoci da gaggawa ba. Labarin ya kara da cewa har yanzun akwai burbushin harsasai a jikinansu da kuma wasu matsalolin lafiya da dama.