Kimanin ‘yan gudun hijirar kasar Mali dubu 20 ne za a canza wa wurin zama daga wani sansani da ke Intikane da ke yankin Tillia a jihar TawaN Nijar kusa da iyaka da Mali, zuwa wani gari mai suna Akadany da ke cikin jihar Maradi a tsakiyar kasar.
Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun yanke shawarar kwashe ‘yan gudun hijirar daga yankin na Tillia ne saboda dalilai na tsaro, musamman ma lura da yadda ake samun yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a yankin da ke daf da kan iyakar kasar da Mali.
Tuni dai aka dakatar da ayyukan jinkai ga ‘yan gudun hijirar dubu 20 da ke zaune a sansanin na Tillia kamar dai yadda mahukunta a yankin suka tabbatar.
Gwamnatin Nijar ta ce, ta yanke wannan shawara ce bayan tattaunawa da jami’an Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR.
A cikin wannan shekara, ‘yan bindiga da ke tsallaka iyaka daga Mali sun kashe kimanin fararen hula 141 a garuruwan da ke yankin na Tillia, kuma tun a wannan lokaci ne gwamnatin Nijar ta ce za ta dauki matakin kare ‘yan kasar daga hare-haren ‘yan bindiga.
Nijar da Mali dai na cikin kasashen afirka da suke fama da matsalar rashin tsaro sakamkon yawaitar kungiyoyin ta’addanci masu tada kayar baya wadanda ake zargin suna samun goyon baya gami ga gudunmawa daga kasashen ketare irin su Faransa da sauran manyan kasashe masu son zuwa nahiyar ta afirka mai yawaitar ma’adanai domin deban dukiya.
Ana sa ran mutanen nahiyar afirka su waye domin tashi su kwaci hyancin su ko sa samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.