Jami’an tsaron hadin guiwa a jihar Niger sun yi nasarar halaka ‘yan bindiga 20 tare da ceto wasu mutum biyar da aka yi garkuwa dasu.
Jami’an tsaron sun kai samame ne kauyen Gaskiya Bana wanda ke da iyaka da jihohin Niger da Kaduna a karamar hukumar Munya ta jihar.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar yace mutum 5 din da aka ceto duk ‘yan asalin kauyen Chukun ne dake Kaduna kuma watansu 1 hannun ‘yan bindiga.
Jami’an rundunar hadin guiwa ta tsaro sun halaka ‘yan bindiga 20 tare da ceto wasu mutum 5 da aka yi garkuwa dasu yayin samamen da suka kai Gaskiya Bana, kauye mai iyaka da jihohin Niger da Kaduna a karamar hukumar Munya ta jihar Niger, jaridar The Nation ta rahoto.
Wadanda aka yi garkuwa dasu din an gano sun kwashe wata daya a hannun ‘yan bindigan.
‘Yan bindigan an gano suna aiki ne da rikakken shugaban masu garkuwa da mutane, Alhaji Leyi, wanda ya kafa dabarsa kuma yake barna a Gaskiya Bana dake karamar hukumar Munya.
Aiki da dakarun suka yi ya kwashe sa’o’i biyar.
Kwamishinan tsaron Niger ya magantu Kwamishinan tsaron cikin gida da walwala, Emmanuel Umar ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yace jami’an sun kutsa maboyar ‘yan bindigan wadanda suka arce tare da barin wadanda suka sace da kuma kudadensu.
Kamar yadda Umar yace, jami’an sun ci karo da wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’addan suka kai musu a Unguwan Aboki amma suka dakile shi tare da halaka wasu ‘yan ta’addan kuma suka saka su dole suka ja da baya.
Kwamishinan ya bayyana sunayen wadanda aka ceto da: Yakubu Abuba, Susan Sunday, Patience Sunday, Lazarus John da Bulus Yahaya inda ya nada da cewa duk wadanda aka sace din daga kauyen Chukun suke na jihar Kaduna.
“Dukkan wadanda aka sace an yi musu bayani tare da sake sada su da iyalansu bayan an duba lafiyarsu.” – Yace.
Ya yabawa kokarin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wurin murkushe lamurran ta’addanci a jihar.
Zamfara: ‘Yan Sanda sun damke ‘yan bindiga 7, Sun Ceto Mutum 15
A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar da damko ‘yan bindiga 7 a raye.
Sun kara da ceto wasu mutum 15 daga sansanonin ‘yan bindiga a jihar.