Gwamna Neysom Wike ya sanar da cewa zai kara nada wasu sabbin mutane 100,000 bayan na farkon da ya nada.
Wike yace yana wadannan nade-nade ne saboda kowa ya samu abinc kuma a sha romon demokradiyya.
Wike ya yi wadannan nade-nade ne a makonnin da suka gabata kuma aikinsu daya; kare kuri’un PDP a 2023.
Gwamna Neysom Wike na jihar Rivers, ya fadada adadin sabbin hadiman akwatunan zabe na musamman zuwa 200,000.
Gwamnan yayi rantsar da sauran hadimai 100,000 da ya nada a baya a filin kwallon Adokiye Amiesimaka dake Omagwa, karamar hukumar Ikwerre jihar Rivers.
Neysom Wike ya rantsar da su ne ranar Juma’a, 4 ga watan Nuwamba, 2022, rahoton TheNation. Ya bayyana cewa dalilin fadada nadin shine amsa kiran wasu mutane da suka bayyana niyyar yi masa aiki.
Yace ya yi wannan ne don cika alkawarin da ya yiwa al’ummar jihar cewa kowa zai samu abinci daga gwamnatin. Ya umurci shugabannin kananan hukumomi su koma yankunansu don sake tattara sunayen mutanen dake bukatar a basu mukami don su samu abinci.
Zuwa N200,000 Legit ta tattaro muku jerin nade-naden da Wike yayi:
1. Nadin mutum 40 matsayin Jami’an Lura na kananan hukumomi ranar 11 ga Oktoba, Wike ya nada mutum 40 matsayin wakilai na kananan hukumomi
2. Nadin mutum 319 matsayin Jami’an Lura na gundumomi Hakazalika a wannan rana, Wike ya nada mutum 319 da zasu lura da kuri’u a gundunomin jihar 319.
3. Nadin masu bashi shawara na musamman na akwatinan zabe 14,359 Ba tare da bata lokaci ba, Wike ya kara nada mutum 14,359 matsayin wadanda zasu lura masa da akwatinan zabe sama da 14,000 dake fadin jihar.
4. Nadin hadimai na musamman guda 50,000 Yayinda aka fara cece-kuce kan nadin, Wike ya kara bada mamaki inda ya sanar da nadin mutum 50,000 matsayin wadanda zasu bashi shawara kan rumfuna da akwatunan zabe a 2023.
5. Fadada Nadin hadimai na musamman zuwa 100,000 Wike a ranar Juma’a, 14 ga Oktoba ya fadada nadin hadiman zuwa 100,000. Ya bayyana hakan ne yayin zaman da yayi da yan jarida a gidan gwamnatin jihar.
Ya bayyana cewa ya cika dukkan alkawuransa na ayyukan ganin da ido tare da matsawa zuwa gina jama’a a fannin siyasar jihar tasa.
Source:legithausang