Gwamnonin Najeriya da masu ruwa da tsaki sun halarci taron NESG na 28 da ake yi a garin Abuja.
A wajen taron, Gwamna Nasir El-Rufai ya yi kira ga gwamnati tayi watsi da tsarin tallafin fetur Gwamnoni sun ce akwai rashin gaskiya a tsarin, kuma kokarin rage farashin mai ya durkusa kas.
Gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bada shawarar a gaggauta cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya take biya.
Vanguard tace Gwamnan ya yi wannan kira ne a wajen taron NESG da ake yi a garin Abuja.
Da aka tambayi gwamnan na jihar Kaduna a kan abin da ya kamata gwamnatin tarayya tayi, sai yace a gaggauta watsi da tsarin tallafin man fetur.
Gwamnan yace gwamnonin jihohin kasar nan 36, jami’an gwamnatin tarayya da majalisar tattalin arziki sun amince a cire tallafin tun Satumban 2021.
An yi watsi da maganar da aka yi Nasir El-Rufai yake cewa ya yi mamaki da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ki dabbaka wannan matsaya duk da matsalar da biyan tallafin ya jawo.
A cewar Gwamnan, daukar nauyin farashin fetur da gwamnatin Najeriya take yi, ya jefa kasar a cikin kalubale, baya ga rashin gaskiya da ake tafkawa.
A rahoton Leadership, an ji El-Rufai da takwarorinsa na Edo da Gombe, Gwamna Inuwa Yahaya da Gwamna Godwin Obaseki sun yi wannan kira.
Gwamnonin jihohin sun ce ya kamata gwamnatin tarayya tayi maza-maza ta dakatar da tsarin biyan tallafin fetur, kuma a inganta wutar lantarki.
A wannan taro wanda shi ne na 28 a tarihi, gwamnonin sun nemi gwamnatin Muhammadu Buhari mai-ci da ta sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya.
El-Rufai ya dage kan harkar man fetur, rahoton yace Mai girma Obaseki ya nuna damuwarsa a kan sha’anin lantarki domin a samu ayyukan yi.
Shi kuma Gwamna Inuwa na jihar Gombe yace ya kamata a canza fasalin kasa ta yadda kowace jiha za ta amfana da bangaren da tayi fice kan ‘yar uwarta.
Za a biya tallafin fetur a 2023? A baya kun ji labari shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna gwamnatin tarayya tana kashe makudan kudi a kan tallafin man fetur duk shekara.
Shugaban kasar yake cewa gwamnatinsa ta batar da N1.5tr a cikin watannin shidan farkon 2022.
Wannan ne ya sa aka cire tallafin daga kasafin kudin badi.