Hukumar da ke kula da samar da wutar lantarki a Nijeriya (NERC) ta sanar da cire dukkanin daraktocin kamfanin rarraba wutar lantarki ta Kaduna (KAEDC) bisa gazawar kamfanin wajen biyan basukan kamfanin NBET ke binta.
Wannan na kunshi ne a cikin wata kundin mai dauke da kwanan wata 1 ga Janairu, dauke da sanya hannun shugaban NERC, Sanusi Garba da mataimakinsa Musiliu Oseni.
Hukumar ta ce matakin ya kuma fara aiki ne tun daga ranar 1 ga Janairu har sai hukumar ta sanar da mataki na gaba.
“Dukkanin daraktocin kamfanin KAEDC an cire su daga ofis, sannan majalisar daraktoci kuma an rushe su bisa dogara da karfin sashi na 75 na dokar wutar lantarki (EA).
“Daga yanzu an nada Dakta Umar Abubakar Hashidu a matsayin jami’in da zai kula da KAEDC bisa dogara da sashin 75 na dokar EA,” a cewar hukumar.
A fadin sanarwar, jami’an shi ne zai kula da harkokin yau da kullum na kamfanin domin tabbatar da komai na tafiya yadda ya dace ba tare da tangarda ba har zuwa lokacin da za a kafa jagororin kamfanin.
Ta kuma ce, zai yi aiki ne tare da daraktoci na musamman da aka kafa wadanda ba daraktoci masu cikakken iko ba ne domin tafiyar da harkokin kamfanin rarraba wutar lantarki ta Kaduna.
“Don haka an nada daraktoci na musamman na l KAEDC: Aled A. Okoh, a matsayin shugaba, Kabir Adamu, Sharfuddeen Zubair Mahmoud, John Ayodele da kuma Rahila Thomas,” NERC ta shaida
Source: LEADERSHIPHAUSA