Bayanai sun fara fitowa daga bakin maharan da aka kama sun shiga gidan Sanatan APC a Jihar Neja.
Wata sanarwa da hukumar yan sandan jihar ta fitar ranar Litinin ta nuna waɗanda ake zargin sun faɗi dalilin zuwa gidan.
Idan baku manta ba wasu mahara sun shiga gidan Sanata Sani Musa, mai wakiltar Neja ta gabas jim kaɗan bayan ya tafi Abuja.
‘Yan bindigan da suka shiga a hannu a gidan Sanatan APC, Muhammad Sani Musa, dake Minna, babban birnin jihar Neja sun fara bayanin wanda ya turo su.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yaadda Sanata Musa, mai wakiltar mazaɓar Neja ta gabas, wanda ke neman tazarce ya tsallake harin yan bindiga a gidansa.
An ce Sanatan ya bar gida zuwa Abuja lokacin da ‘yan ta’addan suka barka cikin gidansa a zatonsu yana nan, Allah ya yi taimako aka rutsa aka kama su.
Wanene ya turo maharan gidan sanatan?
Kakakin yan sandan yace a sabon bayanin da suka yi, waɗanda ake zargi sun ce sun samu labarin Sanatan ya koma jihar Neja ne domin ya halarci bikin naɗi da miƙa sandar mulki ga Sarkin Kagara.
Abiodun ya ƙara da cewa maharan sun ce wani mai suna Sherrif ne ya sanar da su labarin.
Sanarwan tace: “Mun sake samun bayanan gaskiya yayin binciken da muke, ɗaya daga cikin yan bindigan ya amsa laifinsa da cewa ƙarƙashin jagorancin Sharrif, wanda ake nema ruwa a jallo, suka nufi Sanatan a gidansa dake Minna.”
“Maharan sun yi tsammanin cewa yana gida saboda ya halarci bikin naɗin Sarauta a Kagara a ranar da suka je da nufin sace shi.”
Bugu da ƙari, Abiodun yace maharan sun bincike ko ina a gidan yayin da suka yi ɓadda kamar jami’an tsaro da suka je bincike. Ya kara da cewa dakaru sun bazama don kamo ragowar.