Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa hukumar gudanarwa ta Hukumar Haɓaka Arewa-maso-gabas (NEDC) mai wakilai goma sha biyu da su ka haɗa da Daraktan Sashen Harkokin Jinƙai a Ma’aikatar Harkokin Jinƙai Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya, Alhaji Grema Ali.
A sanarwar da mai ba ministar harkokin jinƙai shawara kan aikin jarida, Nneka Ikem Anibeze, ta raba a Abuja a ranar Litinin, an bayyana cewa Buhari ya aika da takarda zuwa ga Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan a ranar 3 ga Mayu, 2023, inda ya buƙaci majalisar da ta amince da naɗin sababbin membobin hukumar gudanarwar.
Shugaban ƙasar ya ce: ‘‘Kamar yadda Sashe na 1, ƙaramin sashe na 2(5)(b) na Dokar Kafa Hukumar Haɓaka Arewa-maso-gabas ta 2017 ya tanadar, ina farin cikin gabatar wa da Majalisar Dattawa mutum 12 da aka zaɓa, kamar yadda aka jero su a nan ƙasa, a matsayin membobin Hukumar Gudanarwa ta Hukumar Haɓaka Arewa-maso-gabas.
Waɗanda aka zaɓa ɗin dai su ne: Lauya Bashir Bukar Baale, Ciyaman (Arewa-maso-gabas, Yobe), Suwaiba Idris Baba, Babbar Darakta, Harkokin Jinƙai (Arewa-maso-gabas, Taraba), Musa Umar Yashi, Babban Daraktan Gudanarwa da Kuɗi (Arewa-maso-gabas, Bauchi), Dakta Isma’ila Nuhu Maksha, Babban Daraktan Ayyuka (Arewa-maso-gabas, Adamawa), da Umar Abubakar Hashidu, Shugaba (Arewa-maso-gabas, Gombe).
Sauran su ne Grema Ali, memba (Arewa-maso-gabas, Borno), Onyeka Gospel-Tony, memba (Kudu-maso-gabas), Hon. Madam Hailmary Ogolo Aipoh, memba (Kudu-maso-kudu), Air Commodore Babatunde Akanbi (ritaya), memba (Kudu-maso-yamma), Mustapha Ahmed Ibrahim, memba (Arewa-maso-yamma), Hadiza Maina, memba (Arewa ta Tsakiya), da wakili daga Ma’aikatar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa ta Tarayya.